{"id":137046,"date":"2021-04-19T12:22:39","date_gmt":"2021-04-19T16:22:39","guid":{"rendered":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/success-stories\/ramzi-ahmed-yousef-wanda-aka-kama-da-laifi\/"},"modified":"2022-05-16T14:42:21","modified_gmt":"2022-05-16T18:42:21","slug":"ramzi-ahmed-yousef-wanda-aka-kama-da-laifi","status":"publish","type":"success-stories","link":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/success-stories\/ramzi-ahmed-yousef-wanda-aka-kama-da-laifi\/","title":{"rendered":"Ramzi Ahmed Yousef (Wanda Aka Kama da Laifi)"},"content":{"rendered":"\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Harin Bam da Mota Kan Cibiyar Kasuwanci ta Duniya a 1993)\u00a0<\/strong>.<\/h2>\n\n<p>RFJ ya ba da ladan dalar Amurka miliyan biyu kan bayani da ya kai ga kama \u0257an ta\u2019addan Pakistan, Ramzi Ahmed Yousef.\u00a0<\/p>\n\n<p>Yousef ne jagoran harin bam da aka yi da mota na 1993 kan Cibiyar Kasuwanci ta Duniya da ke Birnin New York, wanda ya kashe mutum shida tare da raunata wasu fiye da 1,000. \u2018Yan awanni bayan kai harin Yousef ya gudu zuwa Pakistan a jirgi.\u00a0<\/p>\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"130\" height=\"170\" src=\"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/wp-content\/uploads\/2020\/10\/ramzi_yousef.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-35268\"\/><\/figure>\n\n<p>Yousef ya \u0253ulla a Philipphines, inda ya ha\u0257a wani makircin ta\u2019addanci mai sar\u0199a\u0199iya. Yousef ya tsara kashe Fafaroma John Paul II ranar 14 ga watan Janairun 1995 lokacin da jagoran addinin ke ziyara a Philippines, da kuma yun\u0199urin tarwatsa jiragen Amurka 12 a nahiyar Asiya \u2018yan kwanaki bayan haka. An yi wa shirin la\u0199abin \u201cOplan Bojinka,\u201d wani zaurancen Larabci da ke nufin \u201cShirin Tarwatsawa\u201d ko kuma \u201cOperation Big Bang\u201d a Turance.\u00a0\u00a0<\/p>\n\n<p>Kafin su yi nasarar aiwatar da shirinsu, an fatattaki Yousef da wanda ya ha\u0257a baki da shi, Abdul Hakim Ali Hashim Murad har suka tsere daga gidansu na Manila a ranar 6 ga watan Janairun 1995 bayan wasu sinadarai sun tada haya\u0199i da ya fito daga tagar gidan. Yousef ya nemi Murad ya koma gidan ya \u0257auko wata komfutar hannu da kuma tarin bayanai da ka iya tona musu asiri. Sai dai lokacin da Murad ya koma gidan ya gamu da \u2018yan sanda wa\u0257anda tuni suka isa wurin. Da Yousef ya yi tsammanin cewa tabbas an kama Murad, ya gudu zuwa Pakistan.\u00a0<\/p>\n\n<p>A watan Fabarairun 1995, wani mai ba da bayanai, bayan ya ga tallan RFJ bisa wani kwalin ashana sai kuma da ganin yiwuwar samun lada, ya tuntu\u0253i Ofishin Jakadancin Amurka a Pakistan kuma ya ba da ba da bayanin gano wurin da Yousef yake.\u00a0<\/p>\n\n<p>A ranar 7 ga watan Febrarun 1995, hukumomin Pakistan, da taimako daga dakarun musamman na Sashen Tsaro na Difilomasiyyar Ma\u2019aikatar Harkokin Wajen Amurka suka kama Yousef a Islamabad sannan suka tasa \u0199eyarsa zuwa Amurka don ya fuskanci shari\u2019a.\u00a0<\/p>\n\n<p>Daga Satumban 1996 zuwa Janairun 1998, an yi wa Yousef shari\u2019a kuma an tuhume shii da laifukan da ke da ala\u0199a da ta\u2019addanci a shari\u2019o\u2019i uku daban-daban. A ranar 8 ga watan Janairun 1998, wani al\u0199alin gwamnatin tarayya ya yanke masa hukuncin \u0257aurin rai-da-rai da kuma zaman shekara 240 a gidan yari.<\/p>\n","protected":false},"featured_media":35268,"template":"","class_list":["post-137046","success-stories","type-success-stories","status-publish","has-post-thumbnail","hentry"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/success-stories\/137046","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/success-stories"}],"about":[{"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/types\/success-stories"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/media\/35268"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=137046"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}