{"id":137028,"date":"2021-04-20T09:07:44","date_gmt":"2021-04-20T13:07:44","guid":{"rendered":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/success-stories\/hamsiraji-marusi-sali-wanda-ya-mutu\/"},"modified":"2022-05-16T14:33:55","modified_gmt":"2022-05-16T18:33:55","slug":"hamsiraji-marusi-sali-wanda-ya-mutu","status":"publish","type":"success-stories","link":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/success-stories\/hamsiraji-marusi-sali-wanda-ya-mutu\/","title":{"rendered":"Hamsiraji Marusi Sali (Wanda ya mutu)"},"content":{"rendered":"\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Garkuwa da Amurkawa da kuma kashe su a Philippines<\/h2>\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"130\" height=\"170\" src=\"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/wp-content\/uploads\/2020\/10\/hamsiraji_sali.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-35178\"\/><\/figure>\n\n<p>RFJ ya biya ladan dalar Amurka miliyan \u0257aya kan bayanan da aka bayar da suka kai ga gano inda kwamandan \u0199ungiyar Abu Sayyaf (Abu Sayyaf Group &#8211; ASG) yakeHamsiraji Sali.\u00a0<\/p>\n\n<p>Hamsiraji Sali ya saka hannu a garkuwa da Jeffrey Schilling da ASG ta yi ranar 28 ga Agustan 2000, da kuma garkuwa da mutane a ranar 27 ga Mayun 2001 a Dos Palmas. Don ta saki Jeffrey Schilling, ASG ta bu\u0199aci  miliyan 10 na dalar Amurka da kuma sakin \u2018yan ta\u2019adda na \u0199asa da \u0199asa uku da ke gidajen yarin Amurka: maya\u0199in al-\u0198a\u2019ida Ramzi Yousef, da Wali Khan, da Omar Abd al-Rahman, (wanda aka sani da suna \u201cthe Blind Sheikh&#8221; ko &#8220;Makahon Shehu\u201d) wanda shi ne babban malamin \u0199ungiyar ta\u2019addanci ta Masar mai suna al-Gama\u2019at al-Islamiyya.\u00a0\u00a0<\/p>\n\n<p>A ranar 12 ga watan Afrilun 2001, Jeffrey Schilling ya yi nasarar ku\u0253uta lokacin da dakarun Rundunar Sojan Philipphines suka kai samame kan sansanin ASG da ake tsare da shi sannan aka kai shi Amurka.\u00a0<\/p>\n\n<p>A ranar 27 ga watan Mayun 2001, ASG ta yi garkuwa da Amurkawa uku a Tsibirin Dos Palmas da ke Palawan a Philipphines. Amurkawan uku su ne Guillermo Sobero, da kuma ma\u2019aurata \u2018yan mishan, Martin da Gracia Burnham. A ranar 11 ga watan Yunin 2001, kakakin ASG Abu Sabaya ya sanar da cewa an kashe Guillermo Sobero a matsayin \u201ckyautar ranar haihuwa\u201d ga Shugabar Philippines Gloria Macapagal-Arroyo. A ranar 7 ga watan Oktoban 2001, an gano wani \u0199o\u0199on kan mutum a Tsibirin Basilan, wanda aka tabbatar cewa na Guillermo Sobero ne. A watan Yunin 2002, Martin Burnham ya mutu yayin musayar wuta tsakanin sojojin Philipphines da na ASG; an raunata Gracia amma an ceto ta kuma aka mayar da ita Amurka.<\/p>\n\n<p>A Fabarairun 2002, wata tawagar masu yanke hukunci ta gwamnatin Amurka da ke Gundumar Columbia sun samu Sali da laifuka kamar haka: Ha\u0257a baki da ya kai ga kisa, da garkuwa da mutane, da kuma laifuka uku na satar mutane da ta kai ga rasa rai. A ranar 8 ga watan Afrilun 2004, dakarun sintiri na Rundunar Sojan Philipphines ko a turance Philippine Army Scout Rangers, bisa bayanan da wasu suka bayar, sun \u0199addamar da wani samame na kama Sali, wanda aka kashe yayin musayar wuta da sojojin.\u00a0<\/p>\n","protected":false},"featured_media":35178,"template":"","class_list":["post-137028","success-stories","type-success-stories","status-publish","has-post-thumbnail","hentry"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/success-stories\/137028","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/success-stories"}],"about":[{"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/types\/success-stories"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/media\/35178"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=137028"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}