{"id":81356,"date":"2021-07-20T20:16:49","date_gmt":"2021-07-21T00:16:49","guid":{"rendered":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/terrorist-rewards\/harin-da-aka-kai-a-mazaunin-wucin-gadi-na-cibiyar-hul%c9%97ar-jakadanci-na-%c6%99asar-amurka-a-benghazi-da-libiya-ranar-11-12-satumba-2012\/"},"modified":"2022-05-25T12:31:47","modified_gmt":"2022-05-25T16:31:47","slug":"harin-da-aka-kai-a-mazaunin-wucin-gadi-na-cibiyar-hul%c9%97ar-jakadanci-na-%c6%99asar-amurka-a-benghazi-da-libiya-ranar-11-12-satumba-2012","status":"publish","type":"rewards","link":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/rewards\/harin-da-aka-kai-a-mazaunin-wucin-gadi-na-cibiyar-hul%c9%97ar-jakadanci-na-%c6%99asar-amurka-a-benghazi-da-libiya-ranar-11-12-satumba-2012\/","title":{"rendered":"Hari Kan Ofishin Jakadancin Amurka na Wucin Gadi da Ginin Ofishin Amurka"},"content":{"rendered":"\n<p>Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 10 don bayanai kan harin da aka kai wa Ofishin Jakadancin Amurka na Wucin Gadi a Benghazi na Libya. A ranar 11 zuwa 12 na 2012, Amurkawa hu\u0257u \u2013 Jakadan Amurka a Libya John Christopher Stevens, da Jami\u2019in Gudanarwa Sean Smith, da \u0198wararren ka Harkokin Tsaro Glen Anthony Doherty, da Tyrone Snowden Woods \u2013 aka kashe a wani harin ta\u2019addanci kan Ofishin Jakadancin Amurka na Wucin Gadi da Ginin Amurka a Benghazi na Libya. \u2018Yan ta\u2019adda sun kai hare-hare har da kunna wuta, da amfani da makamai masu sarrafa kansu. Da makamin roka a kan gine-ginen biyu, da kuma kai hari kan sojojin Amurka da ke kai \u0257auki tsakanin wuraren. \u0198ari a kan haka, hare-haren sun ji wa dakarun Amurka biyu mummunan rauni, suka raunata \u2018yan kwangilar tsaro na Libya uku, sannan ya jawo lalata wuraren da kuma daina amfani da su.&#13;\n<\/p>\n\n<p>An haifi Jakada John Christopher Stevens mai shekara 52 a arewacin California, kuma ya fara aiki da Ofishin \u0198asashen Waje a 1991. Jakada Stevens ya yi aiki da ofisoshin \u0199asar waje da yawa kuma shi ne Mataimakin Shugaban Jakadanci a Libya daga 2007 zuwa 2009. Daga Maris \u0257in 2011 zuwa Nuwamban 2011, Jakada Stevens ya yi aiki a matsayin Wakili na Musamman a Majalisar Ri\u0199on \u0198warya ta Libya, kuma ya isa birnin Tripoli a watan Mayun 2012 a matsayin Jakadan Amurka a Libya. Kafin ya fara aiki da Ofishin \u0198asashen Waje, Jakada Stevens lauyan \u0199asa da \u0199asa ne a birnin Washington, D.C. Ya koyar da harshen Ingilshi a mastayin \u0257an sa-kai na Peace Corps a Moroco daga 1983 zuwa 1985. Sakatariyar Harkokin Waje Hillary Rodham Clinton ta bayyana Jakada Stevens a matsyain \u201cjajirtacce mutumin kirki, \u0199wararren jami\u2019in difilomasiyya, kuma gwarzon Amurka\u201d.&#13;\n<\/p>\n\n<p>An haifi Sean Smith mai shekara 34 a San Diego, California, kuma ya shiga sojan sama a 1995, inda ya yi aiki a matsayin mai gudaar da sadarwa ta rediyo, kuma mai mu\u0199amin saja. Smith ya fara aiki da Ofishin \u0198asashen Waje a 2002 a matsayin Jami\u2019in Ya\u0257a Labarai, kuma ya yi aiki a ofisoshin \u0199asashen waje da dama, ciki har da Baghdad, da Pretoria, da Montreal, da The Hague. Smith ya yi balaguro zuwa Benghazi a Satumban 2012 don ba da taimako a \u0253angaren sadarwa ga Ofishin Jakadancin Amurka na Wucin Gadi.&#13;\n<\/p>\n\n<p>Glen Anthony Doherty mai shekara 42, an haife shi a Winchester, Massachusetts kuma an \u0257auke shi a matsayin sojan ruwa a na rundunar Navy SEAL a 1995, inda ya yi aiki a Iraq da Afghanistan. Kafin ya zama sojan ruwa, Doherty ya yi aiki a matsayin mai koyar da sulu, ya je makarantar koyon tu\u0199in jirgi, kuma \u0199wararren mai ba da taimakon lafiya ne da tu\u0199in jirgi. A 2005, Doherty ya fara aiki matsayin \u0257an kwangilar tsaro yana ba wa jami\u2019an Amurka tsaro a \u0199asashen waje. Doherty ya je Benghazi a Satumban 2012 don ba wa jami\u2019an Amurka tsaro.&#13;\n<\/p>\n\n<p>An haifi Tyrone Snowden Woods mai shekara 41 a Portland, Oregon kuma ya shafe shekara 20 a matsayin Navy SEAL, inda ya yi aiki da tawaga masu yawa a Somalia, da Iraq, da Afghanistan. Kazalika, Woods tsohon ma\u2019aikacin jinya ne. A 2010, Woods ya fara aiki a matsayin \u0257an kwangilar tsaro, yana ba wa jami\u2019an Amurka tsaro a \u0199asashen waje Ya yi aiki a fa\u0257in duniya wajen ba wa jami\u2019ai tsaro. Woods ya je Benghazi a Satumban 2012 don ba wa jami\u2019an Amurka tsaro.&#13;\n<\/p>\n","protected":false},"featured_media":31793,"menu_order":0,"template":"","hostages-kidnapping":[],"gender":[],"crime-category":[1806],"location-country":[1822],"region":[1823],"election-interference":[],"organization":[],"dprk":[],"cyber":[],"featured-terrorist":[],"class_list":["post-81356","rewards","type-rewards","status-publish","has-post-thumbnail","hentry","crime-category-ayyukan-taaddanci","location-country-libya-hau","region-near-east-north-africa-and-the-middle-east-hau"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/rewards\/81356","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/rewards"}],"about":[{"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/types\/rewards"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/media\/31793"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=81356"}],"wp:term":[{"taxonomy":"hostages-kidnapping","embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/hostages-kidnapping?post=81356"},{"taxonomy":"gender","embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/gender?post=81356"},{"taxonomy":"crime-category","embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/crime-category?post=81356"},{"taxonomy":"location-country","embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/location-country?post=81356"},{"taxonomy":"region","embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/region?post=81356"},{"taxonomy":"election-interference","embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/election-interference?post=81356"},{"taxonomy":"organization","embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/organization?post=81356"},{"taxonomy":"dprk","embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/dprk?post=81356"},{"taxonomy":"cyber","embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/cyber?post=81356"},{"taxonomy":"featured-terrorist","embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/featured-terrorist?post=81356"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}