{"id":183439,"date":"2024-03-26T09:00:00","date_gmt":"2024-03-26T13:00:00","guid":{"rendered":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/rewards\/gungun-yan-kasuwar-aqap\/"},"modified":"2024-05-28T13:10:34","modified_gmt":"2024-05-28T17:10:34","slug":"gungun-yan-kasuwar-aqap","status":"publish","type":"rewards","link":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/rewards\/gungun-yan-kasuwar-aqap\/","title":{"rendered":"Gungun \u2018Yan Kasuwar AQAP"},"content":{"rendered":"\n<p>Lada Don Adalci na ba da tayin ladan da ya kai dala miliyan 10 don samun bayanan da za su kai ga lalata hanyoyin samun ku\u0257in \u0199ungiyar ta\u2019addanci ta Al-Qa&#8217;ida a Zirin \u0198asashen Larabawa (Al-Qa&#8217;ida in the Arabian Peninsula &#8211; AQAP).<\/p>\n\n<p>\u0198ungiyar da ke da mazauni a Yemen, AQAP na samun ku\u0257i ne ta hanyoyi da dama kamar zalinci, safarar man fetur, garkuwa da mutane da safararsu, garkuwa da mutane don neman ku\u0257in fansa, \u0199ungiyoyin agaji na boge, da kuma taimakon mabiya daga \u0199asashen \u0199etare. Shugabannin AQAP sun yi amfani da wa\u0257annan ku\u0257a\u0257e wajen sayen makamai, da horo, da ayyukan ta\u2019addanci, da kuma \u0199wace wasu yankunan Yemen.<\/p>\n\n<p>Ma\u2019aikatar Harkokin Wajen Amurka na mi\u0199o tayin lada don neman bayanai da za su kai ga ganowa da kuma da\u0199ile hanyoyin samun ku\u0257i na AQAP da masu taimaka mata kamar:<\/p>\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Kamfanonin da ke yi wa AQAP hada-hada tsakanin \u0199asa da \u0199asa;<\/li>\n\n\n\n<li>Cibiyoyi ko mutane da ke taimaka wa AQAP wajen kauce wa takukuman da aka saka mata na \u0199asa da \u0199asa;<\/li>\n\n\n\n<li>Sahihan cibiyoyin ku\u0257i da ke yin kasuwanci da AQAP;<\/li>\n\n\n\n<li>Tura ku\u0257a\u0257e da kayan aiki na AQAP;<\/li>\n\n\n\n<li>Masu ba wa AQAP kyautar ku\u0257i ko kuma masu lalubo mata hanyar kasuwanci;<\/li>\n\n\n\n<li>Cibiyoyin ku\u0257i ko kuma wuraren canjin ku\u0257i da ke yi wa AQAP aiki;<\/li>\n\n\n\n<li>Kasuwanci ko ku\u0257a\u0257en zuba jari da AQAP ke juyawa ko kuma masu ba da su;<\/li>\n\n\n\n<li>Shirin neman tallafi ta intanet da AQAP ko wasu ke yi a madadinta;<\/li>\n\n\n\n<li>Lambobin asusu ko kuma adireshin lalitar ku\u0257in intanet da AQAP ke amfani da su wajen tura ku\u0257i da kuma yin kasuwanci;<\/li>\n\n\n\n<li>Haramtattun tsare-tsare da mambobin AQAP ke yi ko magoya bayanta, wa\u0257anda suke sama wa \u0199ungiyar riba.<\/li>\n<\/ul>\n\n<p>AQAP ta \u0253ulla a watan Janairun 2009 bayan \u2018yan ta\u2019addan Yemen da na Saudiyya sun ha\u0257e. Babban \u0199udirin AQAP shi ne kafa daular Musulunci da kuma aiki da shari\u2019a a \u0199asashen Larabawa da yankin Gabas ta Tsakiya baki \u0257aya.\u00a0 AQAP ta kai wa kadarorin Amurka da na \u0199asashen Yamma hari a \u0199asashen Larabawa da sauran \u0199asashe.\u00a0 \u0198ungiyar ta \u0257auki nauyin kai hare-hare da dama, ciki har da na watan Janairun 2015 da ta kai kan ofishin jaridar barkwanci ta Charlie Hebdo a Paris wanda ya kashe mutum 12.<\/p>\n\n<p>AQAP \u0199awar babbar \u0199ungiyar ta\u2019addanci ta al-Qa\u2019ida (AQ) kuma tana aiki ne tare da shugabanninta na duniya don neman mabiya a \u0199asashen Yamma da kuma fa\u0257a\u0257a \u0199awance. Babban amfanin AQAP a wajen AQ shi ne matsayinta na dillaliya a harkokin ku\u0257i tsakanin abokan hul\u0257arta.&#13;\n<\/p>\n\n<p>AQAP ta kai wani harin da bai yi nasara ba kan wani jirgin sama da bam ranar 25 ga watan Disamban 2009, wanda \u0257an ta\u2019adda Umar Farouk Abdulmutallab ya kai. \u0198ungiyar ta kuma \u0253oye bama-bamai a cikin magurzai (printers) da ake shirin kaiwa Amurka a cikin wasu jiragen ruwa biyu a \u0199arshen shekarar 2010; an gano bamabaman kuma aka kwance su ranar 29 ga watan Oktoban 2010 yayin da aka yi zango a wuri biyu.<\/p>\n\n<p>A ranar 19 ga watan Janairu na 2010, Ma\u2019aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana AQAP a matsayin \u0198ungiyar Ta\u2019addanci ta \u0198asar Waje a \u0199ar\u0199shin sashe na 219 na Dokar \u0198aura da Zama \u018aan \u0198asa da aka yi wa kwaskwarima, da kuma ayyana ta \u0198ungiyar Ta\u2019addanci ta Duniya bisa Umarnin Shugaban \u0198asa na Executive Order 13224 da aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon haka, an hana AQAP ta\u0253a dukkan dukiyar da ta mallaka ko kadara da ke \u0199ar\u0199ashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin hul\u0257ar ku\u0257i da AQAP. Laifi ne mutum ya samar ko ya yi yun\u0199urin samarwa ko taimakawa wajen samar wa AQAP kayan aiki.<\/p>\n","protected":false},"featured_media":181318,"menu_order":0,"template":"","hostages-kidnapping":[],"gender":[],"crime-category":[1964],"location-country":[4444],"region":[1823],"election-interference":[],"organization":[],"dprk":[],"cyber":[],"featured-terrorist":[3557],"class_list":["post-183439","rewards","type-rewards","status-publish","has-post-thumbnail","hentry","crime-category-terrorism-financing-hau","location-country-yemen-hau","region-near-east-north-africa-and-the-middle-east-hau","featured-terrorist-show-terrorist-as-featured-on-homepage-hau"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/rewards\/183439","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/rewards"}],"about":[{"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/types\/rewards"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/media\/181318"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=183439"}],"wp:term":[{"taxonomy":"hostages-kidnapping","embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/hostages-kidnapping?post=183439"},{"taxonomy":"gender","embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/gender?post=183439"},{"taxonomy":"crime-category","embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/crime-category?post=183439"},{"taxonomy":"location-country","embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/location-country?post=183439"},{"taxonomy":"region","embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/region?post=183439"},{"taxonomy":"election-interference","embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/election-interference?post=183439"},{"taxonomy":"organization","embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/organization?post=183439"},{"taxonomy":"dprk","embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/dprk?post=183439"},{"taxonomy":"cyber","embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/cyber?post=183439"},{"taxonomy":"featured-terrorist","embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/featured-terrorist?post=183439"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}