{"id":164869,"date":"2022-11-14T05:30:00","date_gmt":"2022-11-14T10:30:00","guid":{"rendered":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/rewards\/hanyoyin-samun-ku%c9%97in-al-shabaab\/"},"modified":"2023-06-13T10:40:56","modified_gmt":"2023-06-13T14:40:56","slug":"hanyoyin-samun-ku%c9%97in-al-shabaab","status":"publish","type":"rewards","link":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/rewards\/hanyoyin-samun-ku%c9%97in-al-shabaab\/","title":{"rendered":"Hanyoyin samun ku\u0257in Al-Shabaab"},"content":{"rendered":"\n<p>Lada Don Adalci na ba da tayin ladan da ya kai dala miliyan 10 don samun bayanan da za su kai ga lalata hanyoyin samun ku\u0257in \u0199ungiyar ta\u2019addanci ta al-Shabaab. Harkokin ku\u0257i na al-Shabaab na taimaka mata wajen ci gaba da ayyuka da kuma \u0257aukar nauyin hare-haren da ka jawo mutuwar dubban fararen hula da kuma jami\u2019an tsaro a Somaliya da \u0199asashe ma\u0199wabta.<\/p>\n\n<p>Al-Shabaab na bin hanyoyin da aka saba da su na ta\u2019addanci wajen \u0257aukar nauyin harkokinta, kamar ba da cin hanci, da \u0199wace, da tura ku\u0257i ta dandalin hawala, da yin garkuwa da mutane don kar\u0253ar ku\u0257in fansa, da halasta ku\u0257in haram, da kuma \u0257ai\u0257aikun mutane, sai dai ita ma ta \u0199ir\u0199iri hanyoyin samun ku\u0257inta na musamman kuma tana \u0199ara dogara da kanta. \u018aaya daga cikin sabbin hanyoyin samun ku\u0257inta shi ne \u0199wace a hannun manyan mutane, da \u2018yan kasuwa, da manoma: amfani da kasuwar ababen hawan da aka yi amfani da su, tura ku\u0257i ta wayar salula, da kuma satar kayan makiyaya. Ta hanyar kama sabbin garuruwa, al-Shabaab kan shiga haramtattun harkoki kamar ha\u0199ar ma\u2019adanai ta \u0253arauniyar hanya da kuma safarar kayayyaki kamar gawayin coal, da tabar wiwi (da take sayar wa \u0199ungiyoyin miyagu), da hauren giwa, da amfanin gona, da kuma sikari. Kazalika, al-Shabaab kan saka wa mutane haraji, da harkokin kasuwanci, da matu\u0199a jirgin ruwa da sauransu, sannan su kar\u0253i ku\u0257a\u0257e daga afanin gona da na gonaki.<\/p>\n\n<p>Ma\u2019aikatar Harkokin Wajen Amurka na ba da tayin lada don samun bayanai da za su kai ga ganowa da kuma kawo \u0199arshen harkokin:&#13;\n<\/p>\n\n<p>&#8211; babbar hanyar samun ku\u0257in al-Shabaab (misali, \u0199wace da kar\u0253ar haraji, safarar haramtattun kayayyaki da makamai, da kasuwancin \u0199wayoyi)<\/p>\n\n<p>&#8211; amfani da ma\u2019adanan \u0199ar\u0199ashin \u0199asa da al-Shabaab ke yi (kamar sare bishiyoyi, da ha\u0199ar ma\u2019adanai, da sumoga)<\/p>\n\n<p>&#8211; gudunmuwa a \u0257ai\u0257aikun mutane ke bayarwa da kuma shige wa al-Shabaab gaba<\/p>\n\n<p>&#8211; babbar hanyar harkokin ku\u0257i da cibiyoyin ku\u0257i ke yi da kuma yin amfani da  fasahohin aika ku\u0257i don turawa ko kuma samun shiga harkokin ku\u0257i na duniya da wasu ke yi a madadi al-Shabaab<\/p>\n\n<p>&#8211; kasuwanci ko hannayen jari da al-Shabaab ta mallaka ko take juyawa ko kuma masu \u0257aukar nauyinta<\/p>\n\n<p>&#8211; ayyukan kamfanonin \u0199asa da \u0199asa da ke da ala\u0199a da al-Shabaab, da ke gudanar hada-hadar ku\u0257i a madadinta (kamar kasuwancin tsofaffin ababen hawa)<\/p>\n\n<p>&#8211; haramtattun harkoki da suka \u0199unshi mambobin al-Shabaab da magoya bayanta, wa\u0257anda ke amfanar da \u0199ungiyar (kamar yin garkuwa don kar\u0253ar ku\u0257in fansa da kuma \u0199wacen kayayyakin makiyaya)<\/p>\n\n<p>&#8211; haramtattun harkokin ku\u0257i na al-Shabaab (kamar halasta ku\u0257in haram), da tura ku\u0257a\u0257e ko kaya da al-Shabaab ke yi zuwa ga \u0199awayenta \u2018yan ta\u2019adda da abokan hul\u0257a<\/p>\n\n<p>Ranar 18 ga watan Maris na 2008, Ma\u2019aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana al-Shabaab a natsayin \u0198ungiyar Ta\u2019addanci ta \u0198asar Waje \u0199ar\u0199ashin sashe na 219 na Dokar \u0198aura da Zama \u018aan \u0198asa, wadda aka yi wa kwaskwarima.\u00a0 Daga baya, a ranar 19 ga watan Maris na 2008 Ma\u2019aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana al-Shabaab a natsayin \u0198ungiyar Ta\u2019addanci ta Duniya bisa Umarnin Shugaban \u0198asa na Executive Order 13224 da aka yi wa kwaskwarima.\u00a0 Sakamakon haka, an hana al-Shabaab ta\u0253a duka dukiya ko kadarori da ta mallaka da ke \u0199ar\u0199ashin ikon Amurka, kuma an haramta wa dukkan Amurkawa yin hul\u0257ar ku\u0257i da al-Shabaab. Laifi ne mutum ya samar ko ya yi yun\u0199urin samarwa ko ya taimaka wajen samar wa al-Shabaab kayan aiki.<\/p>\n","protected":false},"featured_media":162342,"menu_order":0,"template":"","hostages-kidnapping":[],"gender":[],"crime-category":[1964],"location-country":[4436,4431],"region":[1808],"election-interference":[],"organization":[4134],"dprk":[],"cyber":[],"featured-terrorist":[3557],"class_list":["post-164869","rewards","type-rewards","status-publish","has-post-thumbnail","hentry","crime-category-terrorism-financing-hau","location-country-kenya-hau","location-country-somaliya","region-africa-sub-sahara-hau","organization-al-shabaab-hau","featured-terrorist-show-terrorist-as-featured-on-homepage-hau"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/rewards\/164869","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/rewards"}],"about":[{"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/types\/rewards"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/media\/162342"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=164869"}],"wp:term":[{"taxonomy":"hostages-kidnapping","embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/hostages-kidnapping?post=164869"},{"taxonomy":"gender","embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/gender?post=164869"},{"taxonomy":"crime-category","embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/crime-category?post=164869"},{"taxonomy":"location-country","embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/location-country?post=164869"},{"taxonomy":"region","embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/region?post=164869"},{"taxonomy":"election-interference","embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/election-interference?post=164869"},{"taxonomy":"organization","embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/organization?post=164869"},{"taxonomy":"dprk","embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/dprk?post=164869"},{"taxonomy":"cyber","embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/cyber?post=164869"},{"taxonomy":"featured-terrorist","embeddable":true,"href":"https:\/\/38ec3b35-6f9f-491a-bc0d-08b6c6f4d58c.rfj.tips\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/featured-terrorist?post=164869"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}