An kafa Ƙungiyar Neman Sauya Hali ta 17 Nuwamba (Revolutionary Organization 17 November – 17N) a 1975 a matsayin masu tsattsauran ra’ayin kawo sauyi. Ƙungiyar ta nemi korar sansanonin Amurka daga Girka, da korar sojojin Turkiyya daga Cyprus, da yanke alaƙa tsakanin Girka da ƙawancen tsaro na NATO da ƙungiyar Tarayyar Turai. 17N ce ke da hannu wajen kai hare-haren ta’addanci a Girka, ciki har da harbi da harin roka da na bam. Ayyukan ta’addanci na ƙungiyar sun haddasa mutuwar ‘yan Amurka huɗu. William Nordeen, da Ronald Stewart, da George Tsantes, da Richard Welch. Wani ɓangare na 17N ya ɗauki alhakin kai harin ranar 12 ga watan Janairun 2007 da aka kai da makamin gurneti na RPG kan ofishin jakadancin Amurka a Athens.
A ranar 8 ga watan Oktoban 1997, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana 17N a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje ƙarƙashin sashe na 219 na Dokar Ƙaura da Zama Ɗan Ƙasa, wadda aka yi wa kwaskwarima. A ranar 3 ga Satumban 2015, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta janye ayyana 17N matsayin ‘yan ta’adda.
