Ƙungiyar ‘Yanta Yankin Moro ta Ƙasa (Moro National Liberation Front - MNLF)

Gabas da yanKin Pacific

Lada

Ba da gudunmawarka.

An kafa Ƙungiyar ‘Yanta Yankin Moro ta Ƙasa (Moro National Liberation Front – MNLF) a Philippines a shekarar 1972.  Ta fara ne a matsayin wadda ta ɓalle daga ƙungiyar Muslim Independence Movement. MNLF ce babba daga cikin ƙungiyoyin ‘yan aware na Moro na tsawon kusan shekara 20 tun daga shakarun 1970. A farkon shekarun 1990, da yawa daga mambobin MNLF sun ɓalle don kafa Ƙungiyar Abu Sayyaf (Abu Sayyaf Group – ASG), ɗaya daga cikin ƙungiyoyin ta’adda mafiya muni a Philippiines.

A 1996, MNLF ta saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tare da gwamnatin Philippines, inda suka ƙirƙiri yarjejeniyar zaman lafiya da ssuka kira Special Zone of Peace and Development (SZOPAD). An naɗa shugaban MNLF Nur Misuari a matsayin gwamnan yanki mai cin gashin kansa na Autonomous Region of Muslim Mindanao (ARMM), wani yanki da ya ƙunshi gunduma biyu na dandariyar ƙasa da kuma gunduma uku na tsibiri, inda kuma aka bai wa Musulmai mafiya rinjaye ƙwarya-ƙwaryar ‘yancin kai.  Rikice-rikice tsakanin kungiyoyin ‘yan tawaye da jami’an tsaron gwamnati ya ci gaba da wakana a Mindanao, hakan yasa yawancin mazauna yankin suka yi kira domin a kirkiro wani tsari sahihi na cin gashin kai da kawo ci gabagaMusulman Mindanao.

A ranar 29 ga watan Satumban 2009, a tsibirin Jolo da ke Philippines, wani bam da MNLFta saka ya tashi da ayarin motocin soji. Harin ya kashe sojan Amurka biyu da sojan Philippines ɗaya, wadanda ke aikin agaji domin gina makaranta a yankin.

A 2013, wasu masu biyayya ga MNLF sun yi wa birnin Zamboanga ƙawanya tsawon mako uku wanda ya kashe gwamman jami’an tsaron Philippines da ɗaiɗaita dubbai.

A yanzu, MNLF ta ƙunshii ɓangarori da yawa, waɗansu daga ciki sun goyi bayan tattaunawa tsakanin gwamnatin Philippines da kungiyar Moro Islamic Liberation Front (MILF). Tattaunawar ta kai ga amincewa da dokar Bangsamoro Organic Law (BOL) a 2018 da ƙirƙiro yankin Bangsamoro Autonomous Region of Muslim Mindanao (BARMM) a 2019.

Skip to content