Labaran da suka tabbata

Ramzi Ahmed Yousef (Wanda Aka Kama da Laifi)

Harin Bam da Mota Kan Cibiyar Kasuwanci ta Duniya a 1993) .

RFJ ya ba da ladan dalar Amurka miliyan biyu kan bayani da ya kai ga kama ɗan ta’addan Pakistan, Ramzi Ahmed Yousef. 

Yousef ne jagoran harin bam da aka yi da mota na 1993 kan Cibiyar Kasuwanci ta Duniya da ke Birnin New York, wanda ya kashe mutum shida tare da raunata wasu fiye da 1,000. ‘Yan awanni bayan kai harin Yousef ya gudu zuwa Pakistan a jirgi. 

Yousef ya ɓulla a Philipphines, inda ya haɗa wani makircin ta’addanci mai sarƙaƙiya. Yousef ya tsara kashe Fafaroma John Paul II ranar 14 ga watan Janairun 1995 lokacin da jagoran addinin ke ziyara a Philippines, da kuma yunƙurin tarwatsa jiragen Amurka 12 a nahiyar Asiya ‘yan kwanaki bayan haka. An yi wa shirin laƙabin “Oplan Bojinka,” wani zaurancen Larabci da ke nufin “Shirin Tarwatsawa” ko kuma “Operation Big Bang” a Turance.  

Kafin su yi nasarar aiwatar da shirinsu, an fatattaki Yousef da wanda ya haɗa baki da shi, Abdul Hakim Ali Hashim Murad har suka tsere daga gidansu na Manila a ranar 6 ga watan Janairun 1995 bayan wasu sinadarai sun tada hayaƙi da ya fito daga tagar gidan. Yousef ya nemi Murad ya koma gidan ya ɗauko wata komfutar hannu da kuma tarin bayanai da ka iya tona musu asiri. Sai dai lokacin da Murad ya koma gidan ya gamu da ‘yan sanda waɗanda tuni suka isa wurin. Da Yousef ya yi tsammanin cewa tabbas an kama Murad, ya gudu zuwa Pakistan. 

A watan Fabarairun 1995, wani mai ba da bayanai, bayan ya ga tallan RFJ bisa wani kwalin ashana sai kuma da ganin yiwuwar samun lada, ya tuntuɓi Ofishin Jakadancin Amurka a Pakistan kuma ya ba da ba da bayanin gano wurin da Yousef yake. 

A ranar 7 ga watan Febrarun 1995, hukumomin Pakistan, da taimako daga dakarun musamman na Sashen Tsaro na Difilomasiyyar Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka suka kama Yousef a Islamabad sannan suka tasa ƙeyarsa zuwa Amurka don ya fuskanci shari’a. 

Daga Satumban 1996 zuwa Janairun 1998, an yi wa Yousef shari’a kuma an tuhume shii da laifukan da ke da alaƙa da ta’addanci a shari’o’i uku daban-daban. A ranar 8 ga watan Janairun 1998, wani alƙalin gwamnatin tarayya ya yanke masa hukuncin ɗaurin rai-da-rai da kuma zaman shekara 240 a gidan yari.

Skip to content