Kashe Amurkawa.
RFJ ya biya lada ga wani mutum da ya ba da bayanin da ya kai ga kama Mir Aimal Kansi, wani ɗan bindiga da ya harbe kuma ya kashe ma’aikata biyu da kuma raunata wasu mutum uku da ke hanyarsu ta zuwa aiki a hedikwatar hukumar leƙen asiri ta Central Intelligence Agency (CIA) ranar 5 ga watan Janairun 1993.

Kansi ya kai hari ba tare da an tsokane shi ba, ya dinga harba bindigarsa ƙirar AK-47 a kan motocin da ke jira a wata danjar titi da ke gaban ginin babban ofishin Central Intelligence Agency.
Kansi ya gudu daga Amurka jim kaɗan bayan ya kai harin har zuwa lokacin da aka kama shi a 15 ga Janairun 1997 a yankin Punjab na Pakistan. An dawo da shi Amurka don ya fuskanci shari’a.
A ranar 10 ga Nuwamban 1997, tawagar alƙalai ta Fairfax da ke Virginia ta yanke hukunci kan Kansi saboda kisan ma’aikatan CIA din biyu. An zartar wa Kansi hukuncin da kashe shi ranar 14 ga Nuwamba na 2002.
Turo da Bayani
Ba da gudunmawarka. Yi tanadi ga samar da duniyar da ke da zaman lafiya da rayuwa mai kyau nan gaba. Latsa don samun bayani kan hanyoyin tura wa Lada don Adalci bayanai.
- Mutanen da aka yi garkuwa da su/Sace-sacen mutane
- Koriya ta Arewa
- Kutse a Harkokin Zaɓe
