Labaran da suka tabbata

Khadaffy Janjalani (Wanda ya mutu)

Garkuwa da Amurkawa da kuma kashe su a Philippines

RFJ ya biya ladan da ya kai dalar Amurka miliyan biyar ga mutanen da suka ba da bayani kan shugaban ƙungiyar Abu Sayyaf (Abu Sayyaf Group – ASG) Khadaffy Janjalani. A ranar 7 ga watan Yuni na 2007, jakadan Amurka a Philippines ya jagoranci biyan ladar ga mutanen a wajen wani biki a bainar jama’a da ya gudana tsibirin Jolo. 

Khadaffy Janjalani na cikin manyan jagororin ƙungiyar ta’addanci ta ASG a Philippines. Khadaffy Janjalani ne ke da alhakin sacewa da kisan ‘yan ƙasashen Philippines da Amurka. Da shi aka sace Martin da Gracia Burnham da wasu Amurkawa biyu sannan kuma da hannunsa dumu-dumu a sare kan ɗan Amurka Guillermo Sobero. Janjalani ya kuma shirya tare da aiwatar da hare-hare kan kadarorin Amurka, ciki har da manaƙisa kan ofishin jakadancin Amurka a Manila, da kifar da jirgin Superferry 14 a 2004, da kuma dasa bama-bamai uku a Ranar Masoya ko Valentine’s Day, wanda jimilla ya kashe ko kuma raunata ɗaruruwan mutanen da babu ruwansu. 

A ranar 4 ga Satumban 2006, Rundunar Sojan Philipphines, bisa bayanan sirri da mutane da dama suka bayar, ta ƙaddamar da harin kama shi. Yayin hari, rahotanni sun ce an ji wa Janjalani mummunan rauni amma ya tsere. Watanni bayan haka, aka fara yaɗa jita-jitar mutuwar Janjalani. A ƙarshen watan Janairun 2007, mutum biyu suka zo da labarin inda gawar Janjalani take. Bayan kammala gwajin ƙwayoyin halitta, hukumar FBI ta tabbatar da mutuwar Janjalani. Dukkan bayanan da mutanen suka bayar na da matuƙar amfani game da maɓoyarJanjalani da kuma gano shi. 

Skip to content