Garkuwa da Amurkawa da kuma kashe su a Philippines

RFJ ya biya ladan dalar Amurka miliyan ɗaya kan bayanan da aka bayar da suka kai ga gano inda kwamandan ƙungiyar Abu Sayyaf (Abu Sayyaf Group – ASG) yakeHamsiraji Sali.
Hamsiraji Sali ya saka hannu a garkuwa da Jeffrey Schilling da ASG ta yi ranar 28 ga Agustan 2000, da kuma garkuwa da mutane a ranar 27 ga Mayun 2001 a Dos Palmas. Don ta saki Jeffrey Schilling, ASG ta buƙaci miliyan 10 na dalar Amurka da kuma sakin ‘yan ta’adda na ƙasa da ƙasa uku da ke gidajen yarin Amurka: mayaƙin al-Ƙa’ida Ramzi Yousef, da Wali Khan, da Omar Abd al-Rahman, (wanda aka sani da suna “the Blind Sheikh” ko “Makahon Shehu”) wanda shi ne babban malamin ƙungiyar ta’addanci ta Masar mai suna al-Gama’at al-Islamiyya.
A ranar 12 ga watan Afrilun 2001, Jeffrey Schilling ya yi nasarar kuɓuta lokacin da dakarun Rundunar Sojan Philipphines suka kai samame kan sansanin ASG da ake tsare da shi sannan aka kai shi Amurka.
A ranar 27 ga watan Mayun 2001, ASG ta yi garkuwa da Amurkawa uku a Tsibirin Dos Palmas da ke Palawan a Philipphines. Amurkawan uku su ne Guillermo Sobero, da kuma ma’aurata ‘yan mishan, Martin da Gracia Burnham. A ranar 11 ga watan Yunin 2001, kakakin ASG Abu Sabaya ya sanar da cewa an kashe Guillermo Sobero a matsayin “kyautar ranar haihuwa” ga Shugabar Philippines Gloria Macapagal-Arroyo. A ranar 7 ga watan Oktoban 2001, an gano wani ƙoƙon kan mutum a Tsibirin Basilan, wanda aka tabbatar cewa na Guillermo Sobero ne. A watan Yunin 2002, Martin Burnham ya mutu yayin musayar wuta tsakanin sojojin Philipphines da na ASG; an raunata Gracia amma an ceto ta kuma aka mayar da ita Amurka.
A Fabarairun 2002, wata tawagar masu yanke hukunci ta gwamnatin Amurka da ke Gundumar Columbia sun samu Sali da laifuka kamar haka: Haɗa baki da ya kai ga kisa, da garkuwa da mutane, da kuma laifuka uku na satar mutane da ta kai ga rasa rai. A ranar 8 ga watan Afrilun 2004, dakarun sintiri na Rundunar Sojan Philipphines ko a turance Philippine Army Scout Rangers, bisa bayanan da wasu suka bayar, sun ƙaddamar da wani samame na kama Sali, wanda aka kashe yayin musayar wuta da sojojin.
Turo da Bayani
Ba da gudunmawarka. Yi tanadi ga samar da duniyar da ke da zaman lafiya da rayuwa mai kyau nan gaba. Latsa don samun bayani kan hanyoyin tura wa Lada don Adalci bayanai.
- Mutanen da aka yi garkuwa da su/Sace-sacen mutane
- Koriya ta Arewa
- Kutse a Harkokin Zaɓe
