Labaran da suka tabbata

Edgar Gustavo Navarro (Wanda ya rasu)

Garkuwa da Amurkawa a Colombia

RFJ ya biya lada da ya kai na dala Amurka 900,000 ga mutum uku da suka ba da bayanin inda Edgar Navaro yake, wanda shi ne kwamandan ƙungiyar Dakarun Gwagwarmayar Juya Hali na Colombia wato Revolutionary Armed Forces of Colombia (FARC). 

A Fabarairun 2003 FARC ta yi garkuwa daThomas Howes, da Keith Stansell, da Marc Gonsalves lokacin da jirginsu na Amurka ya faɗo a dajin Colombia. FARC da haɗin gwiwar abokan aikinsu sun kashe biyu daga cikin sauran fasinjojin jirgin, ba’amurke Thomas Janis da kuma ɗan Colombia Sergeant Luis Alcides Cruz. 

An zargi Navarro, wanda shi ne mataimakin kwamandan rundunar Teofilo Forero Mobile Column ta FARC, da hannu a garkuwa da mutanen. 

A ranar 19 ga watan Oktoban 2003, wasu mutum uku masu ba da bayanai da ke son samun lada suka jagoranci sojojin Colombia zuwa sansanin da Navarro yake da zimmar kama shi da sauran mambobin FARC. An kashe Navaro yayin musayar wuta da dakarun soja. An ceto Amurkawan uku daga baya a ranar 2 ga watan Yuli na 2008 a wani samame na sojojin Colombia.

Skip to content