Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan Yasin Kilwe, wani jagoran yank na al-Shabaab, wadda Amurka ta ayyana Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasashen Waje. Ana kuma kiran sa da Yasin Usman Kilwe da kuma Yasin Khalid. Kilwe gwamnan al-Shabaab ne a Puntland arewacin Somalia kuma an sha zargin sa da kai hare-hare kan jami’an Puntland.
Kafin shigar sa al-Shabaab, Kilwe ne jagoran wata kungiyar yan’ta’adda a Tsaunukan Galgala da ke arewacin Somaliya. Kungiyar ‘yan ta’addan ta taba karbe iko a tsaunukan da kuma kaddamar da kazamin hari kan wani sansanin sojoji.
A 2012, ‘yan ta’adda magoya bayan Kilwe suka hade da al-Shabaab wacce ta yi mubaya’a ga Al-Ka’ida (Al-Qa’ida – AQ) a wancan lokacin. Wannan hadakar ta taimaka wa al-Shabaab da AQ kara samun karfin dakaru.
