Yasin al-Suri

Nahiyar Near East – Yammacin Afirka da Gabas ta Tsakiya

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 10

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don samun bayanai kan Ezedin Abdel Aziz Khalil, wanda aka fi sani da Yasin al-Suri.

Al-Suri mai samar wa Al-Qa’ida (AQ) da makamai ne wanda yake da zama a Iran. Al-Suri ya yi mu’amalar kudi da kuma daukar sabbin mambobi a fadin Gabas ta-Tsakiya zuwa Iran, sannan zuwa ga Pakistan, duka domin mara baya ga manyan jagororin AQ. Hukumomin Iran sun kyautata huldar dangantaka da al-Suri sannan sun amince masa da ya gudanar da harkoki tsakanin iyakokin Iran tun 2005. A baya, hukumomin Iran sun taba kama Al-Suri a Disamban 2011 bayan sanar da tukwuici na shirin Lada Don Adalci ga duk wanda ya bayar da bayanai da za su taimaka a kamo shi.

A ranar 28 ga watan Yulin, 2011, Ma’aikatar Baitul-Malin Amurka ta ayyana al-Suri a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana al-Suri taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amukawa yin hulɗar kuɗi da shi. Ƙari a kan haka, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya haɗa baki wajen samar wa AQ kayayyaki ko taimako, wadda Amurka ta ayyana Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasashen Waje.

Skip to content