Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan harin bam a Cibiyar Kasuwanci ta Duniya a 1993 a New York City. A ranar 26 ga watan Febrairun, 1993, yan ta’adda suka kai harin bam a cikin mota a wurin ajiye motoci da ke kasan ginin Cibiyar Kasuwanci ta Duniya. Harin ya kashe mutum shida da raunata sama da 1,000 da kuma janyo asarar miliyoyin daloli.

Kungiyar wasu mutane da ke da alaƙa da al-Ka‘ida (AQ) ne wanda ya ƙunshi Abdul Rahman Yasin da Ramzi Yousef suka shirya kai harin. Khalid Sheikh Mohammed, wani babban mamban kungiyar al-Ka’ida kuma kawun Yousef, su ne suka ɗauki nauyin ayyukan. Maharan sun yi fatan cewa bam din zai ruguza bene na farko a cibiyar, inda shi kuma ɓaraguzan ginin zai ruguza gini na biyu. An kama mutum shida daga cikin wadanda suka kai harin, ciki har da jagoran harin Ramzi Yousef, an yi musu shari’a sannan aka yi musu ɗaurin rai-da-rai a gidan yari. Sai dai ba a kama mutum na bakwai da ya kitsa harin ba , Abdul Rahman Yasin.
