Wadoud Muhammad Hafiz al-Turki

Nahiyar Near East – Yammacin Afirka da Gabas ta Tsakiya

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 5

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan Wadoud Muhammad Hafiz al-Turki, wanda aka sani da Sliman Ali Ahmad el-Turki da Bou Baker Muhammad. Ana neman al-Turki wanda mamba ne na Ƙungiyar bau Nidal saboda rawar da ya taka a harin ranar 5 ga Satumban 1986 da ya yi garkuwa da jirgin sama na Pan Am Flight 73 a Karachi, Pakistan. Bayan tsare fasinjoji 379 da ma’aikatan jirgin tsawon awa 16, sai masu garkuwar suka fara harbi kan mai tsautsayi. Mutum 20 ciki har da Amurkawa biyu aka kashe sannan aka raunata fiye da 100.

Wani rukunin masu taimaka wa alƙali a Amurka ya gano laifin al-Turki kuma sunansa na cikin jerin ‘yan ta’addan da FBI ta fi nema. Al-Turki wanda ke shan sigari da yawa, injiniya ne kuma ana kyautata zaton yana zaune a Gabas ta Tsakiya.

Skip to content