Seka Musa Baluku

Afirka – Kudu da Hamadar Sahara

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 5

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dala miliyan biyar don samun bayanai kan jagoran ISIS-DRC Seka Musa Baluku.

A ƙarƙashin jagorancin Seka Musa Baluku, ISIS-DRC ta kai hari da kashewa da aikata fyaɗe da aikata sauran laifukan lalata, haɗi da yin garkuwa da fararen hula, ciki har da yara. Ƙungiyar kan ɗauki yara kuma ta yi amfani da su wajen kai hare-hare da kuma tilasta musu yin ayyuka a lardin Beni na Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC). ISIS-DRC, wadda kuma ake kira Allied Democratic Forces (ADF) da kuma Madina at Tauheed Wau Mujahedeen da wasu sunayen, sun gallaza wa ‘yan Kongo da kuma dakarun haɗin gwiwa na yankin da ke Arewacin Kivu da Ituri a Gabashin ƙasar. Ƙungiyar ta kashe fiye da fararen hula 849 a 2020 kaɗai, a cewar Kwamatin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya.

A watan Maris na 2021, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana Baluku a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya. A daidai lokacin kuma, ma’aikatar ta ayyana ISIS-DRC a matsayin Ƙungiyar Ta’adda ta Ƙasar Waje da kuma Ƙungiyar Ta’addanci ta Duniya.

Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana duk waɗanda aka ayyana taɓa duk wata dukiya da suka mallaka ko kadarori da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amukawa yin duk wata hulɗar kuɗi da su. Duk wasu kamfanonin harkokin kuɗi da suka yi wata hulɗar kuɗi mai yawa da Baluku da gangan a madadin ISIS-DRC za su iya shiga mizanin Amurka ko kuma faɗawa cikin takunkumi. Bugu da ƙari, laif ne wani ya taimaka ta hanyar bai wa ISIS-DRC kayan aiki ko kuma a haɗa baki da shi wajen yunƙurin yin hakan.

A baya Ma’aikatar Baitulmalin Amurka ta saka wa ADF takunkumi, ita ma shi ma Kwamatin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi hakan a 2014 saboda ta’asar da ta aikata. Haka nan, Ma’aikatar Baitulmalin Amurka ta saka wa Baluku takunkumi tare da wasu mambobin ADF a 2019 a ƙarƙashin shirin takunkumi na Global Magnitsky saboda hannunsu a take haƙƙin ɗan Adam. A 2020, Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙara saka wa Baluku wasu takunkuman ta cikin shirin takunkuman DRC.

Skip to content