Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan Sami Jasim Muhammad al-Jaburi, wanda aka sani da Hajji Hamid da Sami Jasim Muhammad al-’Ajuz. Al-Jaburi babban jagora ne a ƙungiyar Daular Islama ta Iraqi da Syria (Islamic State in Iraq and Syria – ISIS) kuma tsohon mamba a al-Qa’ida. Al-Jaburi na taka muhimmiyar rawa wajen kula da harkokin kuɗi na ISIS.
Lokacni da yake matsayin mataimakin shugaban ISIS a kudancin Mosul a 2014, an ruwaito cewa ya yi aiki a matsayin ministan kuɗi na ISIS da ke lura da ayyukan tattara kuɗin shiga ta hanyar sayar da haramtaccen man fetur da gas da kayan tarihi da ma’adanai.
A ranar 29 ga watan Satumban 2015, Ma’aikatar Baitul-Malin Amurka ta ayyana al-Jaburi matsayin Ɗan Ta’addan na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana al-Jaburi taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amukawa yin hulɗar kuɗi da al-Jaburi. Ƙari a kan haka, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya haɗa baki wajen samar wa ISIS kayayyaki ko taimako, wadda Amurka ta ayyana Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasashen Waje.
