Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 1 don bayanai kan Radullan Sahiron, wanda aka sani da Kwamanda Putol. Tun 2005, Sahiron ya kasance babban shugaban ƙungiyar da ke Philippinnes ta Ƙungiyar Abu Sayyaf (Abu Sayyaf Group – ASG), wadda Amurka ta ayyana a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje.
Sahiron ya kai hare-haren ta’addanci da dama ta hayar amfani da bam kan fararen hula da kuma garkuwa da Amurkawa da ‘yan ƙasar waje.
– Sahiron ya ba da umarnin kai harin bam a Tsibirin Jolo a 2004, wanda ya kashe fararen hular Philippines 11 da kuma sojan Amurka ɗaya, sannan ya raunata wasu fiye da 200. Abubuand fashewar da aka dasa an harahaɗa su ne a hedikwatar Sahiron, Camp Tubig Tuh-Tuh da ke Tsibirin Jolo a Philippines. – Sahiron ya taka rawa a garkuwa da mutane a watan Mayun 2001 a Dos Palmas na Amurkawa uku da ‘yan Philippines 17 a wani wurin shaƙatawa na ‘yan yawon buɗe-ido da ke Palawan. An kashe da yawa daga cikin mutanen, har da Ba’amurke Guillermo Sobero. – Ana kallon Sahiron a matsayin babban jagoran harin da aka yi garkuwa da mutane a wurin shaƙatawa na Sipadan, Malaysia a watan Afrilun 2000. Sahiron da wasu mutum huɗu mambobin ASG sun yi garkuwa da ‘yan yawon buɗe-ido 21 ‘yan ƙasar waje, ciki har da Turawan Yamma, da ‘yan Malaysia, da ‘yan Philippines.
Sahiron ya riƙe manyan muƙamai a ASG. Tun daga farkon 1999, ya kasance cikin mutm 14 da ke cikin Majalisar Shura ta ASG. A tsakiyar shekarar 2002, ya yi aiki a matsayin mai ba da shawara ga shugaban ASG Khadaffy Janjalani. Ƙari a kan haka, Sahiron ya riƙe muƙamai da dama wajen gudanar da mayaƙan ASG a yankin Sulu Archipelago na kudancin Philippines. Daga shekarun 2000 zuwa 2003, Sahiron ya riƙe muƙamai a ASG da daban-daban, ciki akwai shugaban sashen Putol na ASG da yake da mambobi aƙalla 100 da suke aii a Tsibirin Jolo a yankin Sulu na kudancin Philippines; a matsayinsa na shugaban ASG a Sulu da ke da ƙungiyoi 18; da matsayinsa na babban kwamandan ASG a Tsibirin Jolo mai mabiya ‘yan bindiga 1,000.
Mai yiwuwa ne Sahiron na ɓoye a kudancin Mindanao ko kuma Patikul Jolo da ke Sulu, Philippines.
A ranar 27 ga watan Fabarairun 2007, wata kotun tarayya a Amurka ta ce Sahiron na da laifi kuma ta tuhume shi da garkuwa da mutane. Hukumomin Amurka sun ba da umarnin kama shi a ranar. Sahiron na cikin jerin ‘yan ta’addan da FBI ta fi nema.
A ranar 30 ga watan Nuwamban 2005, Ma’aikatar Baitul-Malin Amurka ta ayyana Sahiron a matsayin Ɗan Ta’addan na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana Sahiron taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin hulɗar kuɗi da Sahiron. Bugu da ƙari, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya taimaka wajen samar wa ASG kayan aiki da gangan.
