Ousmane Illiassou Djibo

Afirka – Kudu da Hamadar Sahara

Lada

Up to $5 million

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan Ousmane Illiassou Djibo, wanda aka sani da Petit Chapori da Khaled Foulani saboda hannunsa a harin Tongo Tongo na Nijar a 2017.

Djibo jagoran ƙungiyar Islamic State of Iraq and Syria in the Greater Sahara (ISIS-GS) ne da ke ayyukanta a Yankin Menaka na Mali. Djibo tsohon abokin hulɗa ne kuma sojan tsohon shugaban ISIS-GS marigayi Adnan Abu Walid al-Sahrawi (Abu Walid). Djibo ya jagoranci mayaƙan ISIS-GS wajen haɗa wani gungu don yin garkuwa da kuma kai hare-hare kan Turawa a Nijar da kuma ƙasashen yankin. Djibo ya kuma shiga ayyukan hare-hare kan dakarun sojan yankin. Ya jagoranci mayaƙan ISIS-GS wajen kai harin ranar 1 ga watan Yulin 2019 kan sansanin dakarun sojan Nijar a Inates da ke yankin Tillaberi na Nijar ɗin. Ya kuma umarci mayaƙan na ISIS-GS wajen yin garkuwa da sojojin Nijar shida a kusa da Tongo Tongo ranar 14 ga Mayun 2019.

A ranar 4 ga watan Oktoban 2017, a kusa da Tongo Tongo, mayaƙan ISIS-GS suka kai wa dakarun Amurka hari da ke horarwa da ba da shawara da taimaka wa sojojin Nijar a yaƙi da ta’addanci. Harin ya jawo mutuwar sojan Amurka huɗu da na Nijar huɗu. An raunata ƙarin Amurkawa biyu da kuma ‘yan Nijar takwas a harin. A ranar 12 ga Janairun 2018, shugaban ISIS-GS na wancan lokacin Ab Walid ya ɗauki alhakin kai harin.

A ranar 28 ga watan Yunin 2021, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana Abdikadir a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon wannan ayyanawa, baya ga sauran abubuwa, an hana Djibo taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amukawa yin duk wata hulɗar kuɗi da Djibo. Ƙari a kan haka, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya haɗa baki wajen samar wa ISIS-GS kayayyaki ko taimako, wadda Amurka ta ayyana Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasashen Waje.

Skip to content