Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan Murat Karayilan, wanda aka sani da Cemal. Karayilan babban jagora ne a Jam’iyyar Ma’aikata ta Ƙurdawa (Kurdistan Workers’ Party – PKK) kuma shugaban rundunar People’s Defense Forces ta PKK, ɓangaren soja na ƙungiyar. Amurka ta ayyana PKK a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje.
A ranar 14 ga Oktoban 2009, Ma’aikatar Baitul-Malin Amurka ta ayyana Karayilan a matsayin Ɗan Sumogar Ƙwayoyi wato Specially Designated Narcotics Trafficker (SDNK) bisa Dokar Ayyana Ɗan Sumogar Ƙwayoyi na Ƙasar Waje ta Narcotics Kingpin Designation Act (Kingpin Act). Sakamakon wannan ayyanawa, an hana Karayilan taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikokn Amurka, kuma an haramta wa Amurkawa yin duk wata hulɗar kuɗi da Karayilan.
