Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 10 don bayanai da za su kai ga daƙile harkokin kuɗi na na Hizballah. Muhammad Qasim al-Bazzal, wanda aka sani da Mohamad Bazzal and Mu’In, babban jami’in Hizballah ne wanda ayyukansa suka ƙunshi sa ido kan harkokin kuɗi tsakanin Hizballah da Dakarun Tsaro na Neman Sauya Hali na Musulunci – Rundunar Qods (Islamic Revolutionary Guard Corps-Qods Force – IRGC-QF).
Al-Bazzal ya taimaka wajen kafa kamfanin Syria mai suna Talaqi Group sannan ya ci gaba da lura da kamfanonin da ke ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda a ƙasashe, kamar Hokoul S.A.L. Offshore da kuma Nagham Al Hayat. A mastayinsa na shugaban Talaqi Group, al-Bazzal na lura da harkokin kuɗi na kamfanin, da kasuwanci, da mulki, da kuma kwangiloli. Tun daga ƙarshen 2018, al-Bazzal ya yi amfani da Talaqi Group da sauran kamfanoninsa wajen ɗaukar nauyi da shiryawa da kuma yin jigilar fetur ga ƙwayen IRGC-QF. Al-Bazzal ya kuma jagoranci ƙawancen Talaqi Group da ALUMIX na Lebanon don yin jigilar ƙarfen aliminiyon zuwa Iran.
A ranar 20 ga Nuwamban 2018, Ma’aikatar Baitul-Malin Amurka ta ayyana al-Bazzal a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana al-Bazzal taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin hulɗar kuɗi da al-Bazzal. Ƙari a kan haka, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya haɗa baki wajen samar wa Hizballah kayayyaki ko taimako, wadda Amurka ta ayyana Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasashen Waje. A ranar 4 ga Satumban 2019, Ma’aikatar Baitul-Malin Amurka ta ayyana kamfanonin Hokoul S.A.L. Offshore, Talaqi Group, Nagham Al Hayat, and ALUMIX saboda kasancewarsu ƙarƙashin al-Bazzal.
