Shirin Lada Don Adalci na ba da tayin ladan da ya kai dala miliyan 10 don neman bayanai kan Mohamoud Abdi Aden, jagoran al-Shabaab da ya taimaka wajen kai hari kan otel ɗin DusitD2 ranar 15 ga watan Janairun 2019 a Nairobi, Kenya. Yayin harin, mayaƙan al-Shabaab ɗauke da manyan makamai da gurneti da sauran abubuwan fashewa suka kai hari a cibiyar kasuwanci ta DusitD2, wanda ya ƙunshi rukunin gidaje shida mai ɗauke da shaguna da ofisoshi da kuma otel. Aƙalla mutum 21 aka kashe a harin, cikinsu har da Ba’amurke.
A ranar 17 ga watan Oktoban 2022, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana Aden a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya a ƙarƙashin Umarnin Shugaban Ƙasa na 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima.
