Shirin Lada Don Adalci na ba da tayin ladan da ya kai dala miliyan 10 don neman bayanai kan Maalim Ayman, jagoran rundunar Jaysh Ayman, bataliyar al-Shabaab da ta kai hare-haren ta’addanci a Kenya da Somaliya. A ranar 5 ga watan Janairun 2020, ‘yan ta’addan al-Shabaab suka kai hari kan dakarun Kenya da na Amurka a filin jirgi na Manda Bay Airfield tare da kashe ma’aikata haya biyu ‘yan Amurka da kuma wani ƙwararren sojan Amurkar da ke aiki a matsayin mai ba da hannu a filin jirgi. An jikkata wani ma’aikacin da kuma sojojin Amurka biyu a harin.
Maalim Ayman ne ya kitsa harin na Janairun 2020. A watan Nuwamban 2020, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana Ayman a matsayin Babban Ɗan Ta’adda na Duniya ƙarƙashin Umarnin Shugaban Ƙasa na 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima.
Manda Bay sansani ne na sojojin Kenya wanda dakarun Amurka ke amfani da shi wajen horas da sojojin ƙasashen Afirka ta Gabas da ba da taimakon wajen yaƙi da ta’addanci, kai agaji a wuraren rikici, da kuma kare muradan Amurka a yankin.
