Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan kashe-kashen Texas Petroleum (UTP). A ranar 12 ga watan Nuwamban 1997, ma’aikatan UTP na kan hanyarsu ta zuwa wajen aiki a Karachi, Pakistan. Yayin da motarus ke tsallaka gadar da ke zuwa office din UTP, wasu ‘yan bindiga suka fito daga wata jar mota ƙirar Honda Civic sannan suka buɗe musu wuta. An kashe dukkan ma’aikatan Amurkawa tare da direbansu ɗan Pakistan a harin.
Harin ka iya zama na ramuwar gayya saboda ɗaure Mir Aimal Kansi a wata kotun Amurka. Kansi na da hannu a kisan jami’an CIA biyu a 1993 a wajen ginin hukumar da ke Langley, Virginia.
