Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dala miliyan biyar don samun bayanai da za su kai ga kama duk wani mutum kuma a kowace ƙasa, wanda ya kashe Shakeel Khan ko aka haɗa baki da shi ko yin yunƙurin hakan.
Da yammacin ranar 30 ga watan Maris na 2019, mai shagon cin abinci kuma mai izinin zama a Amurka Khan ya gamu da ajalinsa bayan wasu sun kashe shi a ƙofar shagon wurin cin abincinsa da ke Johnson City a New York. Wani ɗan bindiga ne ya harbe Khan daidai lokacin da yake rufe shagon da dare.
Khan mai shekara 50 ɗan asalin yankin Swat ne na Pakistan. Ya sha sukar ‘yan ta’adda a bainar jama’a da ke kai hare-hare a ƙasar.
Ofishin mai shigar da kara na Amurka da ke gundumar Arewacin New York da kuma rundunar hadin gwiwa ta FBI na gudanar da bincike kan kisan nasa.
