Kisan Joel Wesley Shrum

Nahiyar Near East – Yammacin Afirka da Gabas ta Tsakiya

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 5

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don samun bayanai kan kisan ɗan Amurka Joel Shrum. A ranar 18 ga Maris ɗin 2012 wani ɗn bindiga a kan babur ya harbe Shrum mai shekara 29 a kan hanyarsa ta zuwa aiki a Taizz, Yemen. ‘Yan kwanaki bayan harin, ‘yan ta’addan ƙungiyar Al-Qa’ida a Zirin Ƙasashen Larabawa (Al-Qa’ida in the Arabian Peninsula – AQAP) suka ɗauki alhakin kisan.

A lokacin rasuwarsa, Shrum na aiki da International Training and Development Center a matsayin jami’in mulki da kuma malamin Ingilishi. Yana zaune a Yemen da matarsa da kuma yara ƙanana biyu.

Skip to content