Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan biyar don samun bayanai kan kisan Jami’an Ofishin Jakadancin Amurka a Karachi, Pakistan biyu a 1995. A ranar 8 ga watan Maris na 1995, wata farar bas na kan hanyar ta kai ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka a wani wuri lokacin da wata tasi rawaya ta gilma gaban ta a wani wuri mai hada-hada, abin da ya sa dole ta tsaya. Sai kuma wata motar ta hana bas ɗin motsawa. ‘Yan ta’adda sanye da takunkumi kuma ɗauke da makamai suka buɗe wa motar wuta, inda suka kashe ma’aikatan ofishin biyu tare da raunata ɗaya.
