Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan kisan ma’aikatan U.S.Agency for International Development (USAID), John Granville da Abdelrahman Abbas Rahama. A ranar 1 ga Janairun 2008, Granville da Rahama na kan hanyarsu ta komawa gida daga wajen shagalin jajiberin Sabuwar Shekara a Khartoum lokacin da aka harbe su. Ƙungiyoyi biyu ne ne suka ɗauki alhakin kisan: rusasshiyar ƙungiyar Al-Qa’ida a Ƙasashen Kogin Nilu Biyu (Al-Qa’ida in the Land of the Two Niles – AQTN) da kuma Masu Taimakon Tauhidi (Ansar al-Tawhid).

An yi wa mutum biyar shari’a kuma aka ɗure su a tsarin shari’ar Sudan bisa samun hannunsu a kisan. Abdelraouf Abu Zaid Mohamed Hamza, Mohamed Makawi Ibrahim Mohamed, Abdelbasit Alhaj Alhassan Haj Hamad, Mohanad Osman Yousif Mohamed, inda aka yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya, amma sai suka gudu daga gidan yari shekara ɗaya bayan yanke musu hukuncin. An ruwaito cewa Mohanad ya mutu a Somalia watan Mayun 2011. Hukumomin Sudan sun sake kama Abdelraouf. Makawi da Abdelbasit an ci gaba da yawonsu. John Granville mai shekara 33 tsohon mai aikin sa-kai ne na Peace Corps kuma mai bincike a Kamaru. Ya yi ta ayyuka a kudancin Sudan tsawon shekara uku. Ayyukansa sun mayar da hankali ne kan dimokuraɗiyya da harkokin mulki, inda ya raba kayayyakin samar da wutar lantarki fiye da 50,000 don taimaka wa mazauna yankin wajen shirya wa zaɓe. Abdelrahman Abbas Rahama mai shekara 39, ya shafe lokaci yana aiki da USAID tun daga 2004 a matsayin ɗaya daga cikin ‘yan tawagar agajin gaggawa a yankin Darfur, Sudan mai suna USAID Disaster Assistance Response Team. Daga baya ya zama direban USAID a Khartoum na Sudan.
