Junzō Okudaira

Gabas da yanKin Pacific | Nahiyar Near East – Yammacin Afirka da Gabas ta Tsakiya | Turai da Eurasia

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 5

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan Junzō Okudaira saboda hannunsa a harin bam ranar 14 ga Afrilun 1988 a gidan rawa na USO Club da ke Naples, Italiya.. Fashewar ta kashe mutum biyar, ciki har da soja mace Ba’amurkiya sanna ta raunata wasu 15, har da sojojin Amurka maza huɗu. Okudaira wanda mamba ne a Jajayen Dakarun Japan (Japanese Red Army – JRA) ta ‘yan ta’adda, an gano laifinsa a Amurka ranar 9 ga watan Afrilun 1993 kan harin na USO Club. Kuma ana zargin sa da hannu a harin bam na 1987 a mota da aka kai kan Ofishin Jakadancin Amurka a birnin Rome.

Skip to content