Kurdistan Workers’ Party (PKK) (Jam’iyyar Ma’aikata ta Ƙurdawa (Kurdistan Workers’ Party – PKK)), ƙungiyar ‘yan aware ce ta Kurdawa wadda asali take a arewacin Iraqi da kudu maso yammcin Turkiyya. Ƙungiyar da ta ƙunshi Kurdawa ‘yan Turkiyya, ta ƙaddamar da ayyukan tarzoma a 1984. Babban muradin PKK shi ne kafa ƙasa mai ‘yancin kanta a kudu maso gabashin Turkiyya. A farkon shekarun 1990, PKK ta tashi daga ayyuka a ƙauyuka zuwa birane.
PKK ta kauce wa tarzoma daga 1999 har zuwa 2004 lokacin da ɓangaren soja na ƙungiyar mai tsattauran ra’ayi ya karɓi ragama kuma ya sanar da daina aiki da salon tsagaita wuta. A 2009, gwamnatin Turkiyya da PKK sun ci gaba da tattaunawar zaman lafiya. Sai dai kuma tattaunawa ta lalalace bayan PKK ta kai hari a watan Yulin 2011 wanda ya kashe sojojin Turkiyya 13. PKK da gwamnatin Turkiyya sun sha gwabzawa a 2011 da 2012, ciki har da harin da aka kai a 2011 da ya kashe sojojin Turkiyya 24 kuma shi ne lamari mafi muni tun 1993. A 2018, an ruwaito hare-hare daban-daban da PKK ta kai kan sojojin Turkiyya, daga ciki akwai wanda PKK ta ɗauki alhakin kaiwa a watan Nuwamba kan sansanin sojan Turkiyya da ya ritsa da gwamman mutane.
Ranar 8 ga watan Oktoban 1997, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana PKK a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje ƙarƙashin sashe na 219 na Dokar Ƙaura da Zama Ɗan Ƙasa, wadda aka yi wa kwaskwarima. Bayan haka, a ranar 31 ga watan Oktoba na 2001 Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana PKK matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wadda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon haka, an hana PKK taɓa dukkan dukiyar da ta mallaka ko kadarori da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin duk wata hulɗar kasuwanci da PKK. Laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya taimaka a samar wa PKK kayan aiki da gangan.
