Ibrahim al-Banna

Nahiyar Near East – Yammacin Afirka da Gabas ta Tsakiya

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 5

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don samun bayanai kan Ibrahim al-Banna, wanda aka sani da Abu Ayman al-Masri. Al-Banna babban jagora ne a Al-Qa’ida a Zirin Ƙasashen Larabawa (Al-Qa’ida in the Arabian Peninsula – AQAP), wadda Amurka ta ayyana a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje wato Foreign Terrorist Organization (FTO). Yana cikin waɗanda suka kafa AQAP, shi ne tsohon shugaban sashen tsaro na ƙungiyar, kuma ya ba wa jagororin AQAP shawarwarin tsaro. Al-Banna ne mutum na ƙarshe da ya rage a waɗanda suka kafa AQAP.

Cikin wata maƙala da ya wallafa a shafin jaridar AQAP ta Ingilishi a 2010, al-Banna ya siffanta harin ranar 11 ga Satumban 2001 da cewa mai kima kuma ya yi barazanar kai wa Amurkawa hari a faɗin duniya a matsayin martani ga ayyukan Amurka a ƙasashen waje. Kafin ya shiga AQAP, al-Banna ya shugabanci Jihadin Musulunci na Masar a Yemen daga 1996 zuwa 1998 kuma daga baya ya riƙe sashen horo da bayanan sirri na ƙungiyar.

A ranar 3 ga watan Yunin 2017, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana al-Banna a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana al-Banna taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin duk wata hulɗar kuɗi da al-Banna. Bugu da ƙari, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya taimaka wajen samar wa AQAP kayan aiki da gangan.

Skip to content