Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan biyar don samun bayanai kan Husayn Muhammed al-Umari, wana aka sani da Hussein Mohammed al- da Abu Ibrahim. Ana neman Al-Umari ne saboda rawar da ya taka a harin bam na 1982 kan jirgin sama na Pan Am Flight 830. Al-Umari ƙwararren mai haɗa bam ne kuma tsohon shugaban Ƙungiyar 15 May (15 May Organization) ta ta’addanci.
A ranar 11 ga Agustan 1982, wani bam da aka yi imanin al-Umari ne ya haɗa shi ya tashi a cikin jirgin Pan Am Flight 830 ɗauke da fasinja 267 da kuma ma’aikata lokacin da yake tafe daga Tokyo, Japan zuwa Honolulu, Hawaii. Fashewar ta kashe wani ɗan shekara 16 da kuma raunata wasu 16. An gano akwai hannun al-Umari a harin da kuma wasu mutum biyu. Gwamnatin Faransa ma ta ce al-Umari na da hannu a harin bam na 1985 a wurin ajiyar kaya na kantin Marks & Spencer da kuma Leumi Bank.
Al-Umari na da shaidar zama ɗan ƙasar Lebanon kuma ƙila yana zaune a Iraq ko Lebanon. Yana cikin jerin sunayen ‘ya ta’addan da FBI ta fi nema. Ma’aikatar Tsaron Amurka ma na ba da tayin lada da ya kai dala 200,000 don samun bayanai da za su kai ga kama shi.
