Lada Don Adalci na ba da tayin ladan da ya kai dala miliyan 10 don samun bayanan da za su kai ga toshe hanyoyin samun kuɗin ƙungiyar ta’addanci ta Dakarun Neman Sauya Hali na Musulunci (Islamic Revolutionary Guard Corps – IRGC).
Hossein Hatefi Ardakani ɗan ɗan kasuwa ne a Iran da ya taimaka wajen samun fasahohi da kuma safararsu don taimaka wa rundunar IRGC wajen samarwa da sayar da makamai. Tun daga 2014, Adarkani ya yi amfani da kamfanoninsa masu shiga tsakani, cikinsu akwai na Malaysia da Hong Kong da Daular Larabawa, don safarar kayayyakin fasahar Amurka da na ƙasashen duniya masu muhimmanci, da kuma bai wa Iran fasahar don ƙera makamanta. Waɗannan makaman, ciki har da jirage marasa matuƙa Shahed-136 da Shahed-131 (UAV), an ƙera su ne don amfanin IRGC sai kuma aka sayar da su a kasuwannin duniya. Wasu daga cikin UAV ɗin an sayar da su ga rundunar sojin Rasha don kai hare-hare a Ukraine. IRGC ce ke samun kuɗi daga ribar da aka samu ta cinikin makaman.
An gano fasahar da ke yi wa jirgi jagora da Amurka ta samar, wanda kuma Adarkani ya yi safara, a ɓaraguzan jirgin Shahed a Ukraine da wasu wuraren yaƙin. Ƙari kan haka, tawagar Ardakani ta yi safarar fasahar latironi ta Amurka (wanda aka fi sani da HEMTS) da wasu kayayyakin da ake haɗa makami mai linzami, da wasu kayan latironin da ake haɗa makamai.
Kamfanonin da ke Malaysia kuma suke taimaka wa Ardakani sun haɗa da Arta Wave Sdn Bhd, da Integrated Scientific Microwave Technologies, da Tecknologi Merak Sdn Bhd. Waɗannan kamfanoni da ma wasu na da rajista a Kuala Lumpur, Malaysia, da kuma wakilai marasa rajista a Hong Kong. Kamfanonin na matsayin wakilan Ardakani don taimaka masa wajen samun kayayyakin Amurka da na ƙasashen duniya, waɗanda ba za su iya samu ba ta sahihiyar hanya saboda takunkuman Amurka kan IRGC da kuma Iran.
Kamfanonin Daular Larabawa da suka haɗa da na Dubai mai suna Smart Mail Services, da Ring Field FZE, da wasu, an gano cewa su ne ba da bayanan ƙarya game da abin da jiragen ruwa ke ɗauke da shi, don guje wa takunkuman Amurka da na sauran ƙasashe, kuma su yi safarar kayayyaki zuwa IRGC a madadin Ardakani.
Ardakani na kuma yin harkoki a wasu kamfanoni da ke Tehran kamar Kavan Electronics Co, Ltd, da Basamad Electronic Pouya Engineering Co, da Teyf Tadbir Arya Engineering Co.
A ranar 19 ga watan Disamban 2023, Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta bayyana tuhumar da take yi wa Ardakani game da laifukan safarar kayayyakin fasahar Amurka na latironi zuwa ga IRGC. A lokaci guda kuma, Ma’aikatar Baitul-Malin Amurka ta saka Ardakani da wasu mutum 10 cikin jeri na musamman bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na to Executive Order (E.O.) 13382, wanda ke daƙile yaɗuwar makamai masu linzami da kuma yadda ake safararsu. Takunkumin ya haramta wa Amurkawa ko mazauna Amurka yin duk wata hulɗar kuɗi (har da hulɗar kasuwanci a Amurka) da ta ƙunshi duk wata dukiya ta mutanen da aka ayyana.
