Harin ‘Yan Ta’adda Kan Amurkawa a Bangladesh

Kudu da Tsakiyar Asiya

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 5

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan kisan Avijit Roy da kuma hari kan Rafida Bonya Ahmed a Dhaka, Bangladesh.

A ranar 26 ga watan Fabarairun 2015, haifafu Bangaladesh kuma ‘yan Amurka Roy da Ahmed na kan ziyarar a Dhaka da zimmar halartar wani baje-kolin litattafai lokacin da wasu mahara suka kai musu hari da gatari. An kashe Roy a harin. Ahmed ya tsira da raunuka, amma an datse masa yatsa da kuma raunuka da yawa a kansa.

A matsayinsa na marubuci, mai fafutika, Roy ya ƙalubalanci tsattsauran ra’ayi a Bangaladesh ta hanyar yaƙin nema ‘yancin faɗar albarkacin baki. Ya shirya zanga-zangar ƙasa da ƙasa don wayar da kai kan halin da waɗanda ba su damu da addini ba ke ciki a Bangaladesh, kuma sananne ne wajen sukar rashin adalci. An kai masa hari ne kum aka kashe shi saboda yawan maganarsa da kuma gwagwarmaya.

Ansarullah Bangla Team (ABT), wata ƙungiyar ta’addanci ta Bangaladesh, ta ɗauki alhakin kai harin. ABT ta nemi ta saka wa matasa tsattsauran ra’ayi don su kashe waɗanda suke gani a matsayin masu adawa da Musulunci. Jim kaɗan bayan haka, tsohon shugan ƙungiyar al-Ka’ida in the Indian Subcontinent (AQIS), Asim Umar, ya wallafa wani bidiyo da aka yaɗa da ke iƙirarin cewa mabiyan AQIS, ciki har da waɗanda ba a kama ba har yanzu, su ne suka kai harin kan Roy da Ahmed.

A ranar 1 ga Yunin 2016, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana AQIS a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje ƙarƙashin sashe na 219 na Dokar Ƙaura da Zama Ɗan Ƙasa, wadda aka yi wa kwaskwarima. Kafin haka, a ranar 30 ga watan Yunin 2016, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana AQIS a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon wannan ayyanawa, baya ga sauran abubuwa, an hana AQIS taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ta mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin duk wata hulɗar kuɗi da AQIS. Laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya taimaka wajen samar wa AQIS kayan aiki da gangan.

Ana kyautata zaton waɗanda suka kai harin na zaune a Bangaladesh.

Skip to content