Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan harin 2017 da aka kai a Nijar.
A ranar 4 ga watan Oktoban 2017, a kusa da ƙauyen Tongo Tongo na Nijar, wasu ‘yan bindiga masu alaƙa da ISIS A Babbar Sahara (ISIS-Greater Sahara – ISIS-GS) sun yi wa rundunar sojan Amurka ta musamman wadda ke da alhakin horarwa da bai wa sojojin Nijar shawara a yaƙi da ta’addanci, kwanton-ɓauna. Harin ya jawo mutuwar sojan Amurka huɗu da na Nijar huɗu. An raunata ƙarin Amurkawa biyu da kuma ‘yan Nijar takwas a harin. A ranar 12 ga watan Janairun 2018, shugaban ISIS-GS Adnan Abu Walid al-Sahrawi ya ɗauki alhakin kai harin.

