Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan harin bam a jirgin Pan Am Flight 103. A ranar 21 ga Disamban 1988, an tarwatsa jirgin Pan Am Flight 103 ƙirar Boeing 747 yana tsaka da tafiya a daidai Lockerbie, Scotland bayan ya taso daga filin jirgin sama na Heathrow Airport daga Landan zuwa filin jirgi na John F. Kennedy Airport da ke New York, ta hanyar amfani da abin fashewa da aka ɓoye cikin wata jaka. Fashewar ta kashe dukkan fasinja 259 da ma’aikatan da ke ciki, ciki har da Amurka 190 da kuma mazauna Amurkar 11. Harin wanda wani ɗan Libya ya shirya kuma aiwatar, shi ne harin ta’adanci mafi girma kan Amurkawa kafin harin 9 ga Satumban 2001. Har yanzushi ne hari mafi grima a Birtaniya.

Jim kaɗan bayan harin, jami’an tsaron Amurka da na Scotland suka ƙaddamar da binciken haɗɗin gwiwa. A Nuwamban 1991 hukumomi suka gabatar da tuhuma a Amurka da Scotland kan jami’an leƙen asiri na Libya Abdel Baset Ali al-Megrahi da Lamen Khalifa Fhimah.
A ranar 31 ga watan Janairun 2001 aka ɗaure al-Megrahi kan dukkan cajin da aka yi masa, amma aka wanke Fhimah. An yanke wa al-Megrahi hukuncin ɗaurin rai-da-rai. A watan Agustan 2009, an sako shi daga gidan yari saboda dalilan jin-ƙai bayan an gano yana fama da cutar kansa. Al-Megrahi ya rasu a gidansa na Libya a watan Mayun 2012.
A ranar 21 ga Disamban 2020, Ma’aikatar Shari’ar ta Amurka ta sanar da ƙarin tuhuma kan tshohon jami’in leken asiri na Libya, Abu Agela Mas’ud Kheir al-Marimi, saboda hannunsa a harin bam ɗin.
