Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 10 don bayanai da za su kai ga lalata harkokin kuɗi na Hizballah. Hizballah ta dogarad da kuɗin da take samu ta hanyoyi da kuma gungun ƙawance wajen gudanarwa da kuma kai hare-hare a faɗin duniya. Hizballah na samun kusan dala biliyan ɗaya duk shekara ta hanyar taimako kai-tsaye daga Iran, da harkokin kasuwanci na ƙasa da ƙasa, da gungun masu ba da tallafi, da cin hanci, da ayyukan halasta kuɗin haram.
Hizballah na amfani da kuɗaɗe wajen ɗaukar nauyin ayyukan ƙeta a faɗin duniya, ciki har da tura dakarunta Syria don taimaka wa gwamnatin Assad, da zargin ayyukan tattara bayanan sirri a Amurka, da ƙwarewa a ayyukan soja ta yadda Hizballah ke iƙirarin ta mallaki makamai masu linzami. Ana ɗukar nauyin waɗnnan ayyukan ne ta hanyar tallafi daga gungun magoya bayan Hizballah – masu zuba jari da kuma ayyukan raya ƙasa da ke zaman ruhin ƙungiyar. Hizballah na karɓar maƙudan kuɗi da makamai da horo dag Iran, wadda Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana a matsayin Ƙasar da ke Ɗaukar Nauyin Ta’addanci.
A ranar 8 ga watan Oktoban 1997, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana Hizballah a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje ƙarƙashin sashe na 219 na Dokar Ƙaura da Zama Ɗan Ƙasa, wadda aka yi wa kwaskwarima. Bayan haka, a ranar 31 ga watan Oktoba na 2001 Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana Hizballah matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon haka, an hana Hizballah taɓa dukkan dukiya ko kadarori da ta mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin duk wata hulɗar kasuwanci da Hizballah. Laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya taimaka a samar wa Hizballah kayan aiki.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka na ba a tayin lada don samun bayanai da za su kai ga ganowa da kuma kawo ƙarshen harkokin kuɗin:
- Manyan hanyoyin samun kuɗi na ƙungiyar ko kuma manyan masu lalubo mata hanyoyi;
- Manyan masu ba wa Hizballah tallafi da masu lalubo mata hanyoyi;
- Cibiyoyin kuɗi da kuma kasuwannin canjin kuɗi da ke juya wa Hizballah kuɗi d gangan;
- Harkoki da kuɗaɗen zuba jari da Hizballah ta mallaka ko take juyawa;
- Kamfanonin da ke samar da kayayyakin fasaha sakan-han; da
- Haramtattun tsare-tsare da mambobin Hizballah ke aiwatarwa da magoya bayanta, waɗanda ke samar wa ƙungiyar riba.
