Hamad el Khairy

Afirka – Kudu da Hamadar Sahara | Nahiyar Near East – Yammacin Afirka da Gabas ta Tsakiya

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 5

Ba da gudunmawarka.

Sakamakon Adalci na tayin bada ladar da ta kai miliyan $5m domin samar da bayanai kan Hamad el Khairy, wanda kuma aka sani da suna Amada Ould Kheiirou ko Abou Qumqum domin irin rawar da ya taka na zaman sa shugaban day a assasa ƙungiyar ‘yan ta’adda ta Fafutar Haɗin-kai da Jihadi a yankin Afirika ta Yamma (MUJWA).

A ƙarkashin jagorancin Khairy ne ‘yan ƙungiyar ta’addanci ta MUJWA suka kai hare-hare da kuma yin garkuwa da baƙi ‘yan ƙasar waje da masu wasu mutane. Khairy ya yi iƙirarin ɗaukar alhakin garkuwa da aka yi da ‘yan ƙasar Aljeriya ma’aikatan jakadanci a Mali a cikin watan Afirilu 2012, kuma an ga bayanan a cikin fayafayin bidiyon ƙungiyar MUJWA suna barazana ga duk wanda ke adawa da tsarin ƙungiyarsu. A ranar 12 Janairu 2012, Khairy ya bayyana cewa muradin ƙungiyar MUJWA shi ne ta “kafa tsarin shari’ar musulunci ga duk yankunan Afirika ta Yamma”.

Kafin ya kasance shugaban ƙungiyar MUJWA, Khairy ɗan ƙungiyar al-Qa’ida ne a daular Musulunci ta Maghreb kuma ya yi ta kai hare-haren ta’addanci a ƙasar Murtaniya. A watan Okutoba 2011, Khairy ya ba da umurnin a yi garkuwa da turawa uku da wasu ma’aikata a ƙasar Aljeriya, inda mutum biyu suka jikkita sanadiyar harbin bindiga.

A ranar 7 Disamba 2012 ne Sashen Lamurran Ƙasa na ƙasar Amurka ya ayyana Khairy a matsayin Babbabr ƙungiyar Ta’addanci kamar yadda doka mai lamba 13224 ta tanada, kamar yadda dokar ta sauya. Sakamakon wannan ayyanawar da ma wasu abubuwa da suka biyo baya, an rufe duk wasu kadarori da makamantan abubuwa mallakar Khairy waɗanda ke cikin hurumin kasar Amurka, kuma an hana ‘yan ƙasar America baki-ɗaya yin kowace irin hulɗa da Khairy.

Skip to content