Lada Don Adalci na ba da tayin ladan da ya kai dala miliyan 10 don samun bayanan da za su kai ga lalata hanyoyin samun kuɗin ƙungiyar ta’addanci ta Hamas, wadda kuma aka sani da Harakat al-Muqawama al-Islamiya.
Bayan kuɗaɗen da Hamas ke samu daga Iran, hanyoyinta na ɓoye na sama mata kuɗaɗe masu yawa da aka yi ƙiyasin sun kai dala miliyan ɗaruruwa, ta hanyar kamfanonin da ke aiki a Sudan, da Turkiyya, da Daular Larabawa, da sauran ƙasashe.
Hamas tana kuma dogara da ‘yan dalolin da ake ba ta sadaka, kuma ta samu kuɗi ta hanyar neman tallafi a intanet, da kuma kuɗin intanet.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka na ba da tayin lada don neman bayanan da za su kai ga ganowa da dakatar da hanyoyin samun kuɗi na Hamas, da kuma manyan hanyoyin tattara kuɗi da suka ƙunshi:
- Kamfanonin da ke yi wa Hamas hada-hada tsakanin ƙasa da ƙasa;
- Cibiyoyi ko mutane da ke taimaka wa Hamas wajen kauce wa takunkuman da aka saka mata na ƙasa da ƙasa;
- Sahihan cibiyoyin kuɗi da ke yin kasuwanci da Hamas;
- Safarar kuɗaɗe da kayan aiki da Hamas ke yi
- Masu ba wa Hamas kyautar kuɗi ko kuma masu lalubo mata hanyar kasuwanci;
- Cibiyoyin kuɗi ko kuma wuraren canjin kuɗi da ke yi wa Hamas aiki;
- Kasuwanci ko kuɗaɗen zuba jari da Hamas ke juyawa ko kuma masu ba da su;
- Shirin neman tallafi ta intanet da Hamas ke yi ko kuma a madadinta;
- Lambobin asusu ko na lalitar kuɗin intanet da Hamas ke amfani da su wajen tura kuɗi ko kuma kasuwanci; da
- Haramtattun tsare-tsare da mambobin Hamas ko magoya bayanta ke yi, waɗanda suke sama wa ƙungiyar riba.
An kafa Hamas a 1987 a lokacin boren Falasɗinawa na farko ko kuma intifada. Sashen soja na Hamas da ake kira Ɓataliyar Izz al-Din al-Qassam ya kai hare-hare da dama kan Isr’aila da kuma Falasɗinu tun daga shekarun 1990. Waɗannan hare-hare sun ƙunshi manya da ƙanana kan fararen hular Isra’ila da abubuwan fashewa, da kuma hare-haren roka.
Hamas ta ɗauki alhakin kai harin bam na watan Agustan 2001 kan Sbarro a birnin Ƙudus da ya kashe mutum 15, cikinsu akwai Amurkawa biyu, kuma ya raunata fiye da 120.
In April 2016, a Hamas member carried out a suicide attack on a bus in Jerusalem that killed 20 people.
On October 7, 2023, Hamas terrorists launched coordinated attacks from Gaza into Israel which left more than 1,500 innocent civilians – including U.S. citizens – dead and missing. Additionally, Hamas fighters captured more than 200 hostages, including more than a dozen U.S. persons, in that assault and forced them across the border into Gaza.
On October 8, 1997, the U.S. Department of State designated Hamas as a Foreign Terrorist Organization under section 219 of the Immigration and Nationality Act, as amended. Later, on October 31, 2001, the Department of State designated Hamas as a Specially Designated Global Terrorist pursuant to Executive Order 13224, as amended. As a result, all of Hamas’ property, and interests in property, subject to U.S. jurisdiction are blocked, and U.S. persons are generally prohibited from engaging in any transactions with Hamas. It is a crime to knowingly provide, or to attempt or conspire to provide, material support or resources to Hamas.
