Lada Don Adalci na ba da tayin ladan da ya kai dala miliyan 10 don samun bayanan da za su kai ga lalata hanyoyin samun kuɗin ƙungiyar ta’addanci ta Al-Qa’ida a Zirin Ƙasashen Larabawa (Al-Qa’ida in the Arabian Peninsula – AQAP).
Ƙungiyar da ke da mazauni a Yemen, AQAP na samun kuɗi ne ta hanyoyi da dama kamar zalinci, safarar man fetur, garkuwa da mutane da safararsu, garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa, ƙungiyoyin agaji na boge, da kuma taimakon mabiya daga ƙasashen ƙetare. Shugabannin AQAP sun yi amfani da waɗannan kuɗaɗe wajen sayen makamai, da horo, da ayyukan ta’addanci, da kuma ƙwace wasu yankunan Yemen.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka na miƙo tayin lada don neman bayanai da za su kai ga ganowa da kuma daƙile hanyoyin samun kuɗi na AQAP da masu taimaka mata kamar:
- Kamfanonin da ke yi wa AQAP hada-hada tsakanin ƙasa da ƙasa;
- Cibiyoyi ko mutane da ke taimaka wa AQAP wajen kauce wa takukuman da aka saka mata na ƙasa da ƙasa;
- Sahihan cibiyoyin kuɗi da ke yin kasuwanci da AQAP;
- Tura kuɗaɗe da kayan aiki na AQAP;
- Masu ba wa AQAP kyautar kuɗi ko kuma masu lalubo mata hanyar kasuwanci;
- Cibiyoyin kuɗi ko kuma wuraren canjin kuɗi da ke yi wa AQAP aiki;
- Kasuwanci ko kuɗaɗen zuba jari da AQAP ke juyawa ko kuma masu ba da su;
- Shirin neman tallafi ta intanet da AQAP ko wasu ke yi a madadinta;
- Lambobin asusu ko kuma adireshin lalitar kuɗin intanet da AQAP ke amfani da su wajen tura kuɗi da kuma yin kasuwanci;
- Haramtattun tsare-tsare da mambobin AQAP ke yi ko magoya bayanta, waɗanda suke sama wa ƙungiyar riba.
AQAP ta ɓulla a watan Janairun 2009 bayan ‘yan ta’addan Yemen da na Saudiyya sun haɗe. Babban ƙudirin AQAP shi ne kafa daular Musulunci da kuma aiki da shari’a a ƙasashen Larabawa da yankin Gabas ta Tsakiya baki ɗaya. AQAP ta kai wa kadarorin Amurka da na ƙasashen Yamma hari a ƙasashen Larabawa da sauran ƙasashe. Ƙungiyar ta ɗauki nauyin kai hare-hare da dama, ciki har da na watan Janairun 2015 da ta kai kan ofishin jaridar barkwanci ta Charlie Hebdo a Paris wanda ya kashe mutum 12.
AQAP ƙawar babbar ƙungiyar ta’addanci ta al-Qa’ida (AQ) kuma tana aiki ne tare da shugabanninta na duniya don neman mabiya a ƙasashen Yamma da kuma faɗaɗa ƙawance. Babban amfanin AQAP a wajen AQ shi ne matsayinta na dillaliya a harkokin kuɗi tsakanin abokan hulɗarta.
AQAP ta kai wani harin da bai yi nasara ba kan wani jirgin sama da bam ranar 25 ga watan Disamban 2009, wanda ɗan ta’adda Umar Farouk Abdulmutallab ya kai. Ƙungiyar ta kuma ɓoye bama-bamai a cikin magurzai (printers) da ake shirin kaiwa Amurka a cikin wasu jiragen ruwa biyu a ƙarshen shekarar 2010; an gano bamabaman kuma aka kwance su ranar 29 ga watan Oktoban 2010 yayin da aka yi zango a wuri biyu.
A ranar 19 ga watan Janairu na 2010, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana AQAP a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje a ƙarƙshin sashe na 219 na Dokar Ƙaura da Zama Ɗan Ƙasa da aka yi wa kwaskwarima, da kuma ayyana ta Ƙungiyar Ta’addanci ta Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224 da aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon haka, an hana AQAP taɓa dukkan dukiyar da ta mallaka ko kadara da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin hulɗar kuɗi da AQAP. Laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko taimakawa wajen samar wa AQAP kayan aiki.
