Garkuwa da Paul Edwin Overby, Jr

Kudu da Tsakiyar Asiya

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 5

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai da za su kai ga ganowa da dawo da Paul Edwin Overby, Jr gida. A tsakiyar watan Mayun 2014 Overby, wanda marubuci ne ɗan Amurka, ya ɓace a Gundumar Khost da ke Afghanistan lokacin da yake gudanar da bincike kan wani littafi da zai rubuta. Kafin ya ɓata, Overby ya ayyana cewa yana so ya tsallaka zuwa Pakkistan don faɗaɗa binciken nasa. Ganin da aka yi masa na ƙarshe shi ne a Khost City, Afghanistan. Overby na fama da lalurar kunne da ke buƙatar kulawa da ba da magani.

Skip to content