Garkuwa da Mutane da Kashe-Kashe a Lebanon

Nahiyar Near East – Yammacin Afirka da Gabas ta Tsakiya

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 5

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don samun bayanai kan sacewa da kuma kisan Amurkawa a Lebanon daga 1982 zuwa 1992. A tsakanin wannan lokacin, Hizballah da kawayenta ‘yan ta’adda sun yi garkuwa da kusan mutum 100 ‘yan ƙasar waje, akasarinsu Turawa. Daga cikin mutanen, akwai Amurkawa William Buckley, Peter Kilburn, William Higgins waɗanda aka azabtar kuma aka kashe su.

William Buckley ya kasance shugaban ofishin CIA a Lebanon, muƙamin da ya amince ya karɓa bayan harin 1983 kan Ofishin Jakadancin Amurka a Beirut da ya kashe mutum 63, har da Amurkawa 17. A ranar 16 ga watan Maris na 1984 aka yi garkuwa da Buckley a kan hanyarsa ta zuwa wajen aiki. An yi wa Buckley tambayoyi da azabtar da shi kafin ya mutu a hannunsu ranar 3 ga watan Yunin 1985.

Peter Kilburn ya kasance massani a ɗakin karatu na jami’ar American University of Beirut. A 3 ga watan Disamban 1984 aka ba da rahoton ɓacewarsa. Wata 16 bayan haka, an ga gawarsa tare da sauran wasu mutum biyu da aka kama. An harbe mutanen sannan aka yar da gawarwakinsu a kan duwatsun da ke gabashin birnin Beirut.

Higgins na cikin tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya mai kiyaye zaman lafiya a kudancin Lebanon lokacin da aka yi garkuwa da shi ranar 17 ga watan Fabarairun 1988. Masu garkuwa da shi sun binciki Higgins sannan suka azabtar da shi kain daga baya su kashe shi.

Skip to content