Garkuwa da Kuma Kisan William Higgins

Nahiyar Near East – Yammacin Afirka da Gabas ta Tsakiya

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 5

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan sacewa da kuma kashe sojan Amurka Kanar William William Higgins. Higgins na cikin tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya mai kiyaye zaman lafiya a kudancin Lebanon lokacin da aka yi garkuwa da shi ranar 17 ga watan Fabarairun 1988. Masu garkuwa da shi sun binciki Higgins sannan suka azabtar da shi kain daga baya su kashe shi. Higgins na cikin mutum 100 akasarinsu Turawa, waɗanda Hizballah da ‘yan ta’adda ƙawayenta suka yi garkuwa da su lokacin rikicin Lebanon da ya ɗauki tsawon shekaru.

Skip to content