Garkuwa da Kuma Kisan William Buckley

Nahiyar Near East – Yammacin Afirka da Gabas ta Tsakiya

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 5

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan sacewa da kuma kisan William Buckley. Buckley ya kasance shugaban ofishin CIA a Lebanon, muƙamin da ya amince ya karɓa bayan harin 1983 kan Ofishin Jakadancin Amurka a Beirut da ya kashe mutum 63, har da Amurkawa 17. A ranar 16 ga watan Maris na 1984 aka yi garkuwa da Buckley a kan hanyarsa ta zuwa wajen aiki. An yi masa tambayoyi da azabtar da shi kafin ya mutu a hannunsu ranar 3 ga watan Yunin 1985. Buckley na cikin mutum 100 akasarinsu Turawa, waɗanda Hizballah da ‘yan ta’adda ƙawayenta suka yi garkuwa da su lokacin rikicin Lebanon da ya ɗauki tsawon shekaru.

Skip to content