Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan garkuwa da kuma kisan Daniel Pearl. Pearl wanda shi ne Editan Jaridar Wall Street Journal a Kudancin Asiya, an yi garkuwa da shi a Karachi, Pakistan ranar 23 ga Janairun 2002. A Fabarairun 2002, an wallafa wani bidiyo a intanet da ke nuna kisansa. An gano gawar Pearl a watan Mayun 2002 kuma aka kai ta Amurka.
A watan Yunin 2002, an gano laifin Ahmed Omar Saeed Sheikh a Amurka bisa garkuwa da mutum da kuma haɗa bakin wajen garkuwa da mutum, wanda ya kai ga kashe Pearl, da kuma garkuwa da wani Ba’amurken a shekarar 1994. A ranar 15 ga watan Yulin 2002, an kama Sheikh da wasu mutu uku da laifi a Pakistan, inda aka yanke wa Sheikh hukuncin kisa.
A Janairun 2021, Kotun Ƙolin Pakistan ta wanke waɗanda suka aikata garkuwa da Pearl da kuma kashe shi. Amurka na sane da yunƙurin Pakistan na kama Sheikh da laifi kuma tana sane da cewa har yanzu Sheikh na tsare a hannun hukumomin Pakistan. Ana sa ran gwamnatin Pakistan za ta duba zaɓin da take da shi na shari’a don tabbatar da cewa an yi adalci. Kazalika, Amurka ta shirya don tuhumar Sheikh bisa aikin rashin imani da ya yi wa ɗan ƙasar Amurka.

