Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don samun bayanai kan garkuwa da kuma kisan Amurkawa a Colombia a shekarar 2003. A ranar 13 ga watan Fabarairun 2003, wani jrigin Amurka da ke aikin yaƙi da miyagun ƙwayoyi ya yi hatsari a Caqueta, Colombia. Mambobin ‘yan gwagwarmayars neman sauyi a Colombia da ake kira Revolutionary Armed Forces of Colombia (FARC) suka kashe ɗan Amurka Thomas Janis da sojan Colombia Saja Luis Alcides Cruz. ‘Yan tawayen sun kuma yi garkuwa da Amurkawa uku da ke cikin jirgin. Marc Gonsalves, da Thomas Howes, da Keith Stansell.
