Garkuwa da Jirgin Pan Am Flight 73

Kudu da Tsakiyar Asiya | Nahiyar Near East – Yammacin Afirka da Gabas ta Tsakiya

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 5

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan garkuwa da jirgin sama na Pan Am Flight 73. A ranar 5 ga Satumban 1986, mambobin Ƙungiyar Abu Nidal suka yi garkuwa da jirgin Pan Am Flight 73 yayin da yake ajiye a Karachi, Pakistan ɗauke da fasinja 379. Bayan kama fasinjojin da ma’aikata tsawon awa 16, maharan sun fara harbi kan mai tsautayi. Mutum 20 ciki har da Amurkawa biyu aka kashe sannan aka raunata fiye da 100.

An kama mutum biyar da suka kai harin, aka yi musu shari’a tare da yanke musu hukunci a Pakistan. Sai dai kuma, an ruwaito cewa an saki huɗu daga cikinsu a Janairun 2008 kuma yanzu haka suna yawonsu. Wani rukunin masu taimaka wa alƙali a Amurka ya ce kowannensu na da laifi sannan kuma suna cikin jerin ‘yan ta’addan da FBI ta fi nema. Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dala miliyan biyar don samun bayanai kan duka waɗannan mutanen:

  • Wadoud Muhammad Hafiz al-Turki
  • Jamal Saeed Abdul Rahim
  • Muhammad Abdullah Khalil Hussain ar-Rahayyal
  • Muhammad Ahmed al-Munawar

Skip to content