Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai da za su kai ga kama waɗanda suka garkuwa da wani ɗan Amurka, Ihsan Ashour a Bagadaza ranar 13 ga watan Disamban 2019.
Ashour, wanda ke da katin zama a Amurka da Iraqi, yaje Iraqi ne domin yin wasu bukatu na kansa. Yan bindiga akalla 10 ne sanye da takunkumi a fuskokinsu suka yi garkuwa da mutumin a Gundumar al-Sha’ab da ke kusa da Birnin Sadr, yayin wata babbar zanga-zanga a Dandalin Tahrir na babban birnin kasar. Wadanda suka yi garkuwa da mutumin sun lakada masa duka da sanya masa wayoyin wutan lantarki a jiki kafin tafiya da shi zuwa Iran. A cikin Iran, wata kungiyar masu garkuwa ta yi wa Ashour tambayoyi kan ayyukan leƙen asiri da suke gudanarwa. Bayan tantancewa shi ba mai leken asiri ba ne, masu garkuwan sun mayar da shi Iraq, inda aka ci gaba da bincike da kuma azabtar da shi. An sake shi a watan Mayun 2020, inda ya koma gida Amurka.
