Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan Faker Ben Abdelaziz Boussora, wanda kuma aka sani da Abu Yusif al-Tunisi ko Fakeroun. Boussoura ya samu horo daga al-Ka’ida (AQ) wanda ke da burin zama ɗan ƙunar-baƙin-wake. Yana da alaƙa da masu tsattsauran ra’ayin Musulunci kuma abokin wani mamban AQ ne a Tunisia da ake zargi da ta’addanci, Abderraouf Jdey. Boussora ya bar ƙasarsa ta Tunisia a 1988 kuma ya koma Faransa. Ya bar Faransa a 1991 inda ya yi ƙaura zuwa Montreal, Canada, sannan ya yi ta zirga-zirga tsakanin ƙasashen biyu a shekarun 1990. Boussora ya samu shaidar zama ɗan Canada a 1999. A shekarar dai, Boussora ya bar Canada zuwa Afghanistan, inda ya samu horon ta’addanci daga AQ. Daga baya Boussora ya koma Canada. Ba a san ind yake ba yanzu. Hukumomi na cikin damuwa cewa Boussora zai iya komawa Canada ko Amurka don shiryawa ko kuma shiga harin ta’addanci. Babu mamaki yana fama da wata cuta mai tsanani, abin da zai sa ya rage ƙiba sosai ko kuma ya sauya kamanni.
